DUNIYA
1 minti karatu
An yi musayar wuta tsakanin India da Pakistan a rana ta biyu a jere — Rundunar sojan Indiya.
Rundunar ta ce babu rahoton rasa rai, inda ta ce tana mayar da martani ne kan 'yan harbe-harbe da bindigogi "na ba gaira ba dalili".
An yi musayar wuta tsakanin India da Pakistan a rana ta biyu a jere — Rundunar sojan Indiya.
The United Nations has urged the neighbours, who have fought multiple wars in the past, to show "maximum restraint". / AP
26 Afrilu 2025

Sojojin Indiya da na Pakistan sun yi musayar harbe-harbe a daren jiya a kan layin iyaka da ya raba ƙasashen biyu a yankin Kashmir da ake taƙaddama a kai, a karo na biyu a jere, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito, yana ambato rundunar sojin Indiya.

Rundunar sojin Indiya ta ce an yi harbe-harben "na ba gaira ba dalili" daga wurare da dama na sojojin Pakistan "a tsawon layin iyaka a Kashmir" daga daren Asabar zuwa wayewar gari.

"Sojojin Indiya sun mayar da martani yadda ya kamata da ƙananan makamai," in ji sanarwar. "Ba a samu rahoton asarar rai ba."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us