Wasu ‘yan ta’adda da suke da alaƙa da ƙungiyar IS sun buɗe wuta kan masu zaman makoki a wani ƙauye a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, inda suka kashe mutane 15, kamar yadda wani jagoran al’umma ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Talata.
Harin, wanda aka kai ranar Litinin, shi ne na baya bayan nan a jerin hare-hare a yankin, wanda ya ƙara ƙamari a ‘yan makonnin nan.
Fiye da mutane 50 aka kashe a makon jiya.
Mayaƙan ƙungiyar IS a Yammacin Afirka (ISWAP) sun afka wa ƙauyen Kwaple, kusa da ƙauyen Chibok, a kan babura da dama, inda suka buɗe wuta kan jama’ar da suke zaman makokin wani jagoran al’umma a ƙauyen, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.
“A safiyar yau, an gano gawawwaki 15 a ƙauyen da kuma dazukan da suke kewayensa, a cewar Ayuba Alamson, wani jagora a Chibok, kimanin kilomita 15 daga ƙauyen.
“Mayaƙan na ISWAP sun buɗe wa jama’a wuta, sannan suka bi waɗanda suka gudu cikin daji a kan babura,” a cewar Alamson.
Harin na zuwa ne yayin da ‘yan ta’addan Boko Haram ke ƙara tsananta kai hare-hare a yankin Tafkin Chadi
ISWAP, wacce ta ɓalle daga Boko Haram a 2016, ta ƙwace dajin Sambisa a 2021 kuma ta ci gaba da kai hare-hare ƙauyukan da ke kusa da dajin.
A ranar Alhamis, Boko Haram ta kashe manoma 14 a Gwoza, kusa da kan iyaka da Kamaru, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
A makon jiya, Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya shaida wa shugabannin sojoji cewa Boko Haram da abokiyar adawarta ISWAP suna sake tattaruwa a tsibiran gefen Tafkin Chadi, da dajin Sambisa da tsaunukan Mandara a kan iyakar Kamaru, sakamakon “koma bayan da sojoji suka samu”.

Hare-Haren na karshen mako, da suka yi ajalin mutane 22, sun zo ne a lokacin da yankin ke sake shaida dawowar hare-haren ‘yan ta’adda.