Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Burhanettin Duran, ya kai ziyara a hukumance zuwa Burkina Faso a ranakun 13-14 ga watan Mayu domin karfafa dangantakar kasashen biyu da tattauna batutuwan tsaro, kamar yadda majiyoyin Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya suka bayyana.
A yayin ganawarsa a Burkina Faso, Duran ya tattauna kan ci gaban da ake samu a yankin Sahel da Burkina Faso, musamman ma kan yaki da ta'addanci, tare da tattauna dangantakar kasashen biyu da sauran fannoni na hadin gwiwa.
A lokacin ziyarar, Duran ya samu tarba daga Firaimistan Burkina Faso, Jean Emmanuel Ouedraogo, sannan ya tattauna da Ministan Harkokin Waje, Karamoko Jean Marie Traore.
Firaminista Ouedraogo ya jaddada cewa akwai karfin gwiwa daga bangarorin biyu wajen fadadawa da ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Minista Traore ya bayyana cewa Turkiyya abokiya ce mai aminci a lokuta da ake cikin mawuyacin hali, inda ya ce tana bayar da taimako ga Burkina Faso a lokacin da take fuskantar ƙalubale na ta'addanci, kuma Turkiyya ta taka rawa wurin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Burkina Faso da kuma kawar da ta'addanci daga kasar.
Traore ya kara da cewa suna kallon Turkiyya a matsayin kyakkyawar abokiyar hulɗa, kuma suna da niyyar ƙara ƙoƙari wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Ouagadougou da Ankara.
A lokacin ziyarar, an rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda biyu tsakanin ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu.
An amince cewa za a tattauna kan shawarwarin siyasa da za su kunshi dukkan fannoni na dangantakar kasashen biyu a Ankara cikin wannan shekara.