Tsohon kyaftin ɗin tawagar Ingila, kuma tauraron ɗan wasan gaba na Leicester City, Jamie Vardy zai buga wasa na 500 a ƙungiyar da ya yi shekaru 13 yana takawa leda.
Ɗan wasan zai buga wasan a ƙarshen mako, 18 ga Mayu, da Ipswich, maimakon jiran wasan da Leicester za ta buga na ƙarshen kakar bana a gasar Firimiya tare da Bournemouth ran 25 ga Mayu.
Vardy mai shekaru 38 ya faɗa cewa a kakar bana zai bar ƙungiyar bayan shekara 13 tare da su, amma ya kore yiwuwar yin ritaya daga ƙwallo a yanzu.
Tuni dai ta bayyana cewa Leicester City za ta bar gasar Firimiya, saboda rashin tagomashi a bana, inda za ta faɗa ƙaramar gasar Championship.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wasan da Vardy zai buga ranar Lahadi, shi ne wasa na 500 da zai buga mata.
Sauya sheƙa
Tuntuni dai ake raɗe-raɗin cewa Jamie Vardy zai bar Leicester, inda ake alaƙanta shi da ƙungiyoyi kamar Wrexham da ke gasa mai daraja ta biyu a Ingila, da kuma ƙungiyoyin da ke babbar gasar Amurka.
Sai dai rahotannin na cewa Vardy, wanda ya taɓa zama kyaftin ɗin tawagar Ingila, yana ganin yana da sauran nasibi a Firimiya, inda yake fatan komawa wata ƙungiyar da ke buga wasa a gasar.
An ambato shi yana nuna ƙaunarsa ta ci gaba da taka leda a matakin ƙwararru, kasancewar ƙwallo ce burin rayuwarsa tun yana ƙarami.
A yanzu dai ana fatan Jamie Vardy zai ci ƙwallonsa ta 200 a Leicester City a wasan nasa na ƙarshe, sannan za a saurari ganin inda tauraron ɗan wasan zai juya akalar rayuwarsa ta ƙwallo.