Rahotanni game da kocin Real Madrid mai barin gado, Carlo Ancelotti na cewa a halin yanzu ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya na neman naɗa shi kocinta, domin kyautata damarsu ta ɗauko Vinicius Junior daga Madrid.
Bayanan na cewa Al-Hilal za ta miƙa tayin kimanin dala miliyan 900 a bazarar bana don ɗauko Vinicius.
Sai dai batun tafiyar Ancelotti daga Real Madrid batu ne da ke da sarƙaƙiya, duk da ta bayyana cewa yana dab da karɓar aikin horar da tawagar Brazil.
Sai dai sababbin bayanai na nuna cewa zancen ya rushe, wanda har ta sa Al-Hilal a yanzu ta shiga farautar Ancelotti don maye gurbin kocinta, Jorge Jesus.
Shafin Goal ya ambato Sport Zone na cewa Al-Hilal na tunanin cewa nasarar ɗaukar Ancelotti za ta zama silar janyo ra’ayin Vinicius ya zo ƙungiyar tasu.
Zabarin Vinicius
Da ma dai an daɗe ana alaƙanta Vini da ƙaura zuwa Saudiyya kan maƙudan ƙudi, amma ɗan wasan ɗan asalin Brazil yana ta kaucewa.
Ko a yanzu ma rahotannin na cewa Al-Hilal na shirin zuba zunzurutun kuɗin saboda har yanzu Vinicius ne burinsu a kakar sayen ‘yan wasa mai zuwa.
A farkon shekarar nan ne wani tauraron ɗan wasan ɗan Brazil, Neymar Jr, ya bar Al-Hilal ya koma wata ƙungiya a ƙasarsa ta haihuwa.
Al-Hilal na buƙatar ɗauko wani tauraro mai shuhura a duniyar ƙwallo don maye gurbin Neymar.