NIJERIYA
1 minti karatu
An samu sassaucin hauhawar farashin kayayyaki a Afrilu a Nijeriya – NBS
A sabuwar ƙididdigar da NBS ɗin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu raguwa daga kaso 24.23 da yake a Maris zuwa 23.71 a watan Afrilu.
An samu sassaucin hauhawar farashin kayayyaki a Afrilu a Nijeriya – NBS
Haka kuma a binciken da NBS ɗin ta yi a matakin shekara, an samu raguwa a hauhawar farashi daga kaso 38.80 cikin 100 a watan Disamba zuwa 24.48 a watan Janairu. / Reuters
15 Mayu 2025

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar da sabbin bayanan ƙididdiga inda ta bayyana cewa an samu raguwar tashin farashin kayayyaki a ƙasar.

A sabuwar ƙididdigar da NBS ɗin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu raguwa daga kaso 24.23 da yake a Maris zuwa 23.71 a watan Afrilun 2025.

A bara ne dai aka samu hauhawar farashin da aka shafe gomman shekaru ba a samu irinsa ba a ƙasar biyo bayan matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka na karya darajar naira da kuma cire tallafin man fetur a lokacin da ya hau mulki a 2023.

Haka kuma a binciken da NBS ɗin ta yi a matakin shekara, an samu raguwa a hauhawar farashi daga kaso 38.80 cikin 100 a watan Disamba zuwa 24.48 a watan Janairu.

An ƙara samun raguwa a watan Fabrairu kafin ya ƙaru a Maris.

Wani rahoto da NBS ɗin ta fitar ya nuna cewa a kayayyakin abinci da kuma barasa ne aka fi samun hawa da saukar farashi.

A watan Maris, hauhawar farashin kayan abinci na kan 21.79 inda a watan Afrilu ya sauka zuwa 21.26.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us