NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamna Zulum ya haramta sayar da giya a Borno, ya zargi jami’an tsaro da yada mugayen laifuka
Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka kamar tsaurin ra’ayi da karuwanci da sauran munanan ɗabi’u, lamarin da ke kara ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar.
Gwamna Zulum ya haramta sayar da giya a Borno, ya zargi jami’an tsaro da yada mugayen laifuka
Borno Governor Zulum / Others
7 Mayu 2025

Gwamnan jihar Borno a arewacin Nijeriya, Farfesa Babagana Zulum, ya haramta sayar da barasa, yayin da ya zargi sojoji da sauran jami’an tsaro da aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a birnin Maiduguri da kewaye.

Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu da suke aiki sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka kamar tsaurin ra’ayi da karuwanci da sauran munanan ɗabi’u, lamarin da ke kara ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen kaddamar da wani kwamitin da aka kafa don “ƙwace haramtattun otal-otal da gidajen karuwai da gidajen kwana da maɓoyar miyagun laifuka da kuma daƙile illolin munanan dabi’u.

“Na yi farin ciki da sanin cewa jami’an soji suna wajen nan, musamman sojoji, ‘yan sanda, da sauran su, domin yawancin wadannan ayyukan wa ke yin su? Wasu daga cikinsu akwai jami’an soji da aka kora da masu ci a yanzu har da fararen hula.

"Don haka, bai kamata a ƙi sukar kowane ɓangare ba a cikin wannan lamarin idan har muna son babban birnin Maiduguri da kuma jihar ta kawar da ta'addanci da sauran laifuka," in ji Zulum.

A takaitaccen taron, Zulum ya sake kafa kwamitin tare da sake ba wa kwamitin damar kawar da duk wani nau'i na miyagun laifuka da munanan dabi'u a cikin babban birnin Maiduguri da kewaye.

Dokar hana sayar da barasa da kayan maye, a cewar gwamnan, ta samo asali ne daga yadda ake ta samun tashe-tashen hankula a tsakanin kungiyoyin da ke gaba da juna da kungiyoyin asiri da karuwanci da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ‘yan fashi da sata, wadanda suka haddasa asarar rayuka da dukiya.

Gwamnan ya hada hannu da sojoji, ‘yan sanda, Civil Defence, da wasu jami’an tsaro da dama da suka hada da civilian JTF domin shiga cikin kwamitin domin gudanar da cikakken bincike.

Da yake amincewa da aikin da ke gaban kwamitin da aka sake kafawa, shugaban kwamitin ya yi tir da tabarbarewar harkokin tsaron cikin gida a Maiduguri tare da bayyana matakin da kwamitin zai dauka nan take.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us