Ghana ta tabbatar da isowar kashin farko na ‘yan Yammacin Afirka da aka kora daga Amurka a ƙarƙashin yarjejeniyar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaba John Mahama, wanda ya tabbatar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar Jubilee House ranar Laraba, ya ce mutum 14 ne jirgin sama ya kai ƙasar a wani ɓangare na yarjejeniyar.
Yawancinsu ‘yan Nijeriya ne, yayin da ɗaya daga cikinsu ɗan ƙasar Gambiya ne.
"Hukumomin Amurka sun yi mana tayin karɓar ‘yan wasu ƙasashe da ake so a fitar daga ƙasarsu sannan muka amince cewa za mu karɓi ‘yan Yammacin Afirka saboda dukkan ‘yan’uwanmu na Yammacin Afirka ba sa buƙatar izinin shiga ƙasarmu. Saboda haka idan sun zaɓi tafiya daga Amurka zuwa Accra ba sa buƙatar izinin shiga ƙasar. Saboda haka idan za ka dawo da ‘yan’uwanmu na Yammacin Afirka, ya yi daidai," in ji Shugaban ƙasar.
Ya ƙara da cewa Ghana ta taimaka wajen mayar da ‘yan Nijeriya ƙasarsu ta hanyar ba da motar bas da za ta kai su gida.
Ɗan ƙasar Gambiya kuwa, yana buƙatar a tattauna da ofishin jakadancin ƙasarsu domin samar da tikitin jirgin mayar da shi gida.
Shugaba Mahama ya jaddada cewa shigar Ghana lamarin yana daidai da yarjejeniyar ƙungiyar ECOWAS ta ‘yancin tafiya a cikin ƙasashenta wadda ta bai wa ‘yan ƙasashen ‘yancin iya shiga da kuma zama a cikin wasu ƙasashen Afirka ta Yamma ba tare da biza ba har na tsawon kwanaki 90.
“Afirka ta Yamma na da yarjejeniyar ‘yancin tafiye-tafiye, saboda haka ko wane ɗan Yammacin Afirka yana da ‘yancin zuwa Ghana kuma ya iya zaman kwanaki 90. Saboda haka idan suna dawowa da ‘yan’uwanmu, ba mu da wata matsala wajen karɓarsu,” in ji shi.