DUNIYA
1 minti karatu
Operation Bunyan-un-Marsoos: Ƙarin bayani kan harin ramuwar gayya da Pakistan ta ƙaddamar kan India
Pakistan ta sanar da ƙaddamar da harin ramuwar gayya kan India wanda ta yi wa laƙabi da Operation Bunyan-un-Marsoos, domin mayar da martani kan hare-hare na makamai masu linzami da take kai mata.
Operation Bunyan-un-Marsoos: Ƙarin bayani kan harin ramuwar gayya da Pakistan ta ƙaddamar kan India
Pakistan da Indiya na ci gaba da kai wa juna hare-hare / AA
10 Mayu 2025

Pakistan ta ce ta ƙaddamar da hare-hare na ramuwar gayya wanda ta yi wa laƙabi da Operation “Bunyan-un-Marsoos” kan Indiya bayan New Delhi ta harba mata makamai masu linzami a sansanoninta.

“An fara operation Bunyan-un-Marsoos,” kamar yadda kafar watsa labaran Pakistan ta ruwaito.

“Ana kai hare-hare kan wurare da dama a Indiya domin ramuwar gayya.”

“Bunyan-un-Marsoos” na nufin “gini mai ƙarfi” ko kuma “bangon da ba a iya rusawa.”

Pakistan ɗin ta ce wuraren da ta kai harin sun haɗa da wani wurin ajiye makamai masu linzami ƙirar Brahmos da kuma sansanonin sojin sama da ke pathankot da Udhampur a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin Indiya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito majiyar sojojin Indiya na cewa a halin yanzu Indiya na ci gaba da kai hare-hare ta sama a cikin Pakistan.

An ji ƙarar fashewar abubuwa masu ƙarfi a wurare da dama a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya, kamar yadda mazauna yankin suka ce.        

Fashewar da aka ji a ranar Asabar, an ji ta ne a biranen biyu na Kashmir masu girma na Srinagar da Jammu da sai kuma garin nan da ke da ganuwa wato Udhampur.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us