Daga Dwomoh-Doyen Benjamin
Suna llallabawa ta kan iyakoki da daddare ko a boye da tsakar rana - motocin akori kura dauke da sukari, mai, shinkafa, kayan magunguna da suaran kayayyaki, suna ketare cibiyoyin fito da biyan haraji.
Wadannan ba kasuwanci ba ne da ake yin su a sirrance, kasuwanci ne da ke janyo asarar biliyoyin daloli ga tattalin arzikin kasashen Afirka, matsalar da ke dakile kasuwanci a kasashen, kuma cikin sirri hakan na raunata kasa.
Fasa-kaurin kayayyaki musamman a iyakokin Yammacin Afirka da suke a bude, aiki ne da ake tsara wa, mummunan aiki da ke barazanar rusa tattalin arziki da tsaron kasashe.
A Ghana, inda Kungiyar Masu Samar da Kayayyaki ta Afirka ke jagorantar yaki da fasa-kauri, karara ana iya ganin sakamako. Masu shigar da kaya ta hanyar da ta kamata na shiga garari.
Wasu daga masu zuba jari da aka gayyata zuwa kasar don su samar da ayyukan yi na ficewa, suna bayyana gogayya ta rashin adalci da yanayin kkasuwanci da ke fama da ayyukan da suka saba da dokoki.
Wani hasashe da Hukumar Tattara Haraji ta Ghana ta gudanar ya ce kasar na yin asarar kimanin dala miliyan 720 a kowace shekara saboda fasa-kauri - kudin da za a iya amfani da su wajen manyan ayyuka a fannonin lafiya, ko ilimi.
Amma wannan ba matsalar Ghana ba ce kawai. A fadin Afirka, masu fasa-kauri na amfani da hukumomi masu rauni, tsarin rashawa, da iyakokin da ba su da tsaro don nakasa tattalin arziki.
Suna kirkirar kasuwannin bayan fage da ke da kayan da suka saba ka’ida, yawanci marasa inganci ko masu cutarwa ma da ake sayar da su ga jama’a.
Wata mace mai kasuwanci a Agbobloshie, Ghana ta bayyana yadda man da ake warewa don amfanin masana’antu ke shigowa kasuwar inda wasu ke sayen sa saboda fasa-kauri.
A lokuta da yawa, wadannan kaya da ake fasa-kaurinsu na kassara masu samar da su a cikin gida da masu shigo da su ta halastacciyar hanya, ana raba su da kasuwancinsu da ruguza tattalin arziki mai kyau.
Wani rahoto da Bankin Cigaban Afirka ya fitar, ya bayyana cewa kasashen Afirka na yin asarar kimanin dala biliyan 30 zuwa biliyan 50 a kowacce shekara saboda haramtaccen kasuwanci da fasa-kauri. Ana rasa ayyuka, ana kin biyan haraji, da amincewa da tsarin.
Tasirin hakan a dogon zango na d amuni sosai: karancin zuba jari, karin rashin ayyukan yi, da daduwar gibi tsakanin manufofin cigaban kasa da asalin natijar da za a samu.
A watan Maris din 2025, Sakatariyar Hukumar Kula da Iyakokin Kenya da ma’aikatar Ayyukan Gona sun bayar da rahoton samun tan 2,000 na sukari da aka yi fasa-kaurinsa zuwa kasar a cikin motocin akori-kura da kananan ababan hawa a garin Garissa.
Sun yi gargadin cewa jama’ar yankunan na amfani da kayayyakin da ba su da inganci, wanda ke barazana ga lafiya, kuma ba su wuce ta gaban Hukumat Tabbatar da Ingancin Kayayyaki ta Kenya ba. gwajin da masu hada magunguna suka yi ya tabbatar da kwace sukari da ba a yar da shigo da shi ba, wanda a cikinsu akwai guba.
Tun 2018, Sakataren Harkokin Cikin Gida Fred Matiangi ya bayyana damuwar cewa miliyoyin ‘yan kasar Kenya na iya shan wani sukari mai guba da aka boye ake fitar da shi a matsayin na cikin gida. Wannan ya kawo damuwa sosai ga kasashen Afirka da dama da ke ayyuka a wannan bangare.
Abu mafi muni, ba wai talakawa ne suke fasa-kaurin kayayyakin ba - wasu gungun bata-gari ne aikata hakan wadanda suke da kudade kuma suka san manya.
Wadannan mutane na sace kudaden kasa, na kauce wa takunkumai, kuma suna yawan amfani da ribar da suke samu wajen daukar nauyin mummunan kasuwanci, ciki har da safarar makamai da mutane. Rikicin fasa-kaurin ya zama barazana ga tsaron kasa, ba wai matsala ga tattalin arziki.
Manyan kayayyakin da aka fi fasa-kaurin su a iyakokin kasashen Afirka su ne - man fetur, sukari, man girki, magunguna da shinkafa - kuma kungiyoyin bata-gari ne ke aikata hakan ta iyakokinsu da ba su da tsaro, raunanan jami’an tabbatar da dokoki, da ma alfarmar siyasa.
A bayanin ENACT Africa, sun bayyana cewa man da ake fasa-kauri daga Nijeriya, ana bi da shi ta Kamaru zuwa ‘yan tawayen Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya inda kasar ke yin asarar kimanin dala biliyan 1.5 kowanne wata saboda fasa-kaurin man fetur.
A 2015 Reuters sun bayar da rahoton da ya ce Al Shabaab na samun kusan dala miliyan 1.9 kowace shekara daga fasa-kaurin sukari ta hanyar amfani da sansanin ‘yan gudun hijira na Dadaab da ke Kenya.
Rahoton ya ce wannan kiyasi ya shafi Dadaab ne kasai kuma bai hada da hanyoyin fasa-kauri na Garissa da Wajir ba, wanda hakan ke nufin adadin kudin na iya fin hakan.
Tasirin wannan abu na da yawa sosai. Baya ga rikicin lafiya ga ‘yan Afirka da yadda ake amfani da kudin fasa-kauri don daukar nauyin ta’addanci, a lokacin da gwamnatocin Afirka suka gaza karbar isasshen haraji saboda fasa-kauri, sai su koma rancen kudade daga waje, wanda ke kara yawan bashin da ake bin gwamnati.
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya ya bayyana cewa basussukan da ake bin kasashen Afirka ya kai dala biliyan 702 a 2021, wani bangare mai yawa na da alaka da rasa kudaden shiga saboda munanan ayyuka irin su fasa-kauri.
Fasa-kauri na kuma dakushe manufofin kasuwanci da cigaba. Dama tuni masana’antun yankunan ke fama da tsadar kayayyaki da rashin kayan aiki - gogayya marar adalci na shake su.
Misali a Ghana, kamfanonin sarrafa manja da yawa sun sallami ma’aikata ko sun rufe kamfanonin gaba daya saboda fasa-kaurin kayayyaki marasa inganci masu arha.
Kungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya ta ce bangaren sarrafa shinkafar ya yi asarar dala miliyan 300 saboda fasa-kauri, da cin dunduniyar shoirin gwamnati na dogaro d akai wajen samar da abinci.
A lokacin da aka tankwara kasuwansu suka rufe ko rage ayyuka saboda gogayyar da babu adalci, matasa da ke ta neman ayyuka za su rasa damarmaki.
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa rashin aikin yi a tsakanin matasa a Afirka ya kai kusan kashi 60, alkaluman da ke kira da lallai a dauki matakan gaggawa na sauyi a fannin tattalin arziki da kuma gaggawar kawo karshen kasuwanci marar amfani.
Idan ba a dauki wani kwakkwaran mataki ba nan da nan, lamarin zai kawo karyewar zuciya a tsawon lokaci, kuma za a hankada dukkan ajama’a zuwa ga layin karshe na talauci.
Kungiyar Masu Samar da Kayayyaki ta Afirka (ACCP), ta hanyar gangamin yaki da fasa-kauri da take yi a Gahna da ma Afirka baki daya, na wayar da kan jama’a da farkar da kungiyoyin farar hula, kungiyoyin ‘yan kasuwa, da mahukunta.
Daga tattaunawa da jama’a a da aka yi zuwa ga binciken jarida na kwakwaf, ACCP ta shirya kawar da shirin da jama’a ke yi idan suka ga masu fasa-kauri.
Amma ba za su iya yin hakan su kadai ba, dole ne gwamnatoci su karfafa iyakokinsu d sanya idanu, tabbatar da aiki da dokokin fito da hukunta duk wadanda ke da hannu a wan abu.
Kungiyoyin yankuna da ma Yarjejeniyar AfCFTA, dole ne su yi a fage sama da na kasuwanci, su shiga kasashe su kulla kasuwanci tare da zuba jari a kamfanonin tsaro na hadin gwiwa, su mayar da tsarin haraji iri guda da samar da dakarun yaki da fasa-kauri a yankunan.
Dole ne a karfafa gwiwa masu sayen kayayyaki, ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma don gano wa bayar da rahotannin kasuwanci da ba ya bisa doka.
Makomar Afirka ta dogara ne a kan gaskiya, tafiya da kowa a kasuwanci mai tsafta.
Duk jaka guda na buhun sukarin da aka yo fasa-kaurinsa, dk wata jarka ta man fetur da aka sato, duk wani buhu na shinkafar da ba a biya harajinta, hakan ya zama satar arzikin dan Afirka da ake aimi, cin amanar manufofin habaka masana’antu, da kuma zama barazan ga dorewar dimokuradiyya.
Yanzu ne lokacin d aya kamata a dauki mataki. Fasa-kaurin kayayyaki ba abu ne boyayye ba. Yana nan tattare da mu a ko’ina - na sace kudin kasashenmu a makance. Idan har ba mu dauki mataki ba, to za mu ci gaba da tafka babbar asarar kudade da rayuka.
Marubuci Dwomoh-Doyen Benjamin ne Daraktan Zartarwa na Cibiyar Samar da Kayayyaki ta Afirka (ACCP).
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.