An ji ƙarar fashewar wani abu a tashar ruwa ta Shahid Rajaee da ke birnin Bandar Abbas da ke kudancin Iran a ranar Asabar, inda aƙalla mutum 115 suka jikkata bayan fashewar, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito.
Fashewar ta faru ne a daidai lokacin da Iran ta fara zagaye na uku na tattaunawar da take yi ta nukiliya da Amurka a Oman, duk da cewa a halin yanzu ba a san me ya jawo fashewar ba.
“Abin da ya jawo lamarin shi ne fashewar wasu kwantenoni da dama da aka ajiye a tashar Shahid Rajaee. A halin yanzu muna ƙoƙari kwashe mutanen da suka jikkata zuwa asibitoci,” kamar yadda wani jami’i ya shaida wa kafar talabijin ta ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim shi ma ya ruwaito cewa tuni aka dakatar da hada-hada a tashar ruwan domin samun damar kashe wutar.
Haka kuma ta ce sakamakon yadda tashar ruwan ke da ma’aikata da dama, akwai yiwuwar mutane da dama sun jikkata waɗansu kuma sun rasu.
Rahotanni sun ce tagogin gidajen da ke da nisan kilomita bakwai daga tashar ruwan sun fashe sakamakon ƙarfin fashewar.
Haka kuma daga nesa ana iya ganin yadda hayaƙi ya yi gajimare ya dunƙule a sararin samaniya.