TURKIYYA
2 minti karatu
Masana kimiyyar Turkiyya sun kirkiri na’urar sauti da ke gano ciwon dajin huhu da wuri
Nazari ya bayyana cewa manhajar na gano ciwon dajin huhu da wuri kuma cikin nasara da ta kai kashi 90.
Masana kimiyyar Turkiyya sun kirkiri na’urar sauti da ke gano ciwon dajin huhu da wuri
Bayan aiki na kusan shekara daya da rabi, mun samu kai wa ga tudun mun tsira," in ji Dr Haydar Ankishan / AA
16 awanni baya

Malaman kimiyyar Turkiyya sun samar da wata manhaja da ke samun taimakon ƙirƙirarriyar basira wajen gano ciwon dajin huhu ta hanyar nazari kan muryar mutum.

Tawagar malaman da Dokta Haydar Ankishan daga cibiyar Binciken Ƙwayoyin Halitta ta Jami’ar Ankara, tare da haɗin gwiwar masana daga fannoni daban-daban, shirin na da manufar gano ciwon daji na huhu da wuri, wanda ba a cika gano shi ba sai ya girma.

Da yake bayani ga ‘yan jaridu, Ankishan ya ce: “A nazarinmu, muna kallon yanayin sautin mutum, sannan mu kalli yadda halittar huhu take, da kuma yadda tsarin ke juyawa, sai muka gano sautin zai iya bayar da bayani da haske kan ciwon dajin huhu.”

“Bayan aiki na kusan shekara guda, mun samu sakamako mai kyau, kwalliya ta biya kuɗin sabulu,” in ji shi.

Manhajar na bayar da gargaɗi game da ciwon daji

“Mun gano cewa ciwon daji na huhu, musamman a farkonsa, za a iya gano shi sosai da kashi 90,” in ji shi.

Dr. Bulent Mustafa Yenigun, wanda ke koyarwa a Tsangayar Likitanci ta Jami’ar Ankara wanda na daga cikin masu binciken, ya ce babban abu mai muhimmanci shi ne gano cutar da wuri.

“Mun yi nazarinmu tare da marasa lafiya 50 da masu lafiya 50,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa “An shirya wani rubutu na karantawa ga kowanne mara lafiya don nazari kan murya, an kuma naɗi muryoyiyinsu.”

Da yake bayyana cewa duka sautin da aka naɗa an yi nazari a kan su a matsayin tagwaye, ya ce “Manhajarmu na gano sauyi a murya tare da yin gargadin cewa za a iya samun ciwon dajin huhu.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us