Daga Mazhun Idris da Shamsiyya Hamza Ibrahim
Watan Ramadan a Musulunci wata ne mai alfarma da a acikinsa ake aiwatar da tarin al'adu don tsarkake rai da gangar jiki.
Duk da cewa azumi ya ƙunshi nisantar cin abinci, akwai ɓagaren ɗawainiya a Ramadan a duk inda masu azumntarsa suke. Al’adar buɗa-baki, wato cin abinci lokacin shan-ruwa bayan faɗuwar rana a duka ranakun azumi, tana bambanta daga wuri zuwa wuri a duniya.
Ga mutanen Hausa na Nijeriya, Nijar, da Ghana, da kuma waɗanda ke ƙasashen waje, teburin iftar ɗinsu yakan ƙunshi bajintar al'adu, tarihi, da kayan abinci da suka samo asali daga al'adu.
A irin waɗannan tarukan iftar, akwai haɗin da aka fi so – Kunu da Kosai – wanda yake ƙayatarwa da ɗanɗano mai gamsarwa, ga masu hali ko marasa hali.
Kosai, ga waɗanda ba su saba da shi ba, wani irin abinci ne da ake yi daga wake da aka niƙa, sannan aka soya shi har ya yi ƙarau-ƙarau, kuma akan ci shi da miya ko kuma yaji mai kayan ƙamshi.
Kunu, ɗaya cikin abincin al'ada, wani irin abin-sha ne da ake yi daga gero, dawa, shinkafa, ko alkama tare da ƙarin kayan ƙamshi, tsamiya, ko gyaɗa.
Kunu da Kosai, ko wani nau’in kamar Koko da Kosai (wanda waus ke kira Kose ko Akara), suna bayar da cikakkiyar gamsarwa a matsayin abincin buɗa-baki, yayin da kuma suke nuna al'adun yankin da kuma gadonsu.
A yawancin gidajen Hausa, Kunu da Kosai sukan zo da farko yayin buɗa-baki, kafin sauran kayan abinci su biyo baya.
Mabiya Al'ada
A gidajen Hausa yara sukan tashi su ga iyayensu suna haɗa Kunu da Kosai don karin kumallo, wanda wannan al'ada ake gadar da ita daga ƙarni zuwa ƙarni.
Sinadaran da ake amfani da su wajen yin Kunun Tsamiya, wanda shi ne mafi shaharar nau'in Kunu, ba su da yawa kuma suna da sauƙin samu. Tushen haɗa Kunu shi ne gari da aka dama da ruwan ɗumi.
Ana iya ƙara kayan ƙamshi kamar citta, kaninfari, ko masoro a cikin ruwan kafin a tace ruwan tsamiya a haɗa shi da wannan cakuda.
Mataki na gaba shi ne zuba ruwan zafi sosai a cikin cakuda har sai ya yi kauri. Dangane da yadda ake so, ana iya ƙara ruwan zafi don sarrafa kaurin. Ana ƙara sukari da wani lokaci madara don ɗanɗano.
A cikin al'ummar Hausa, yayin iftar, bayan an bude baki da dabino kamar yadda addinin Musulunci ya ba da shawara, Kunu yawanci shi ne abu na farko da ake ci, kuma ana yawan bai wa baƙi shi donmin yin maraba da kuma karamci.
Gina Jiki
Ko da zafi ko ɗumi, Kunu yana da farin jini tsakanin tsofaffi da matasa a cikin al'ummar Hausa saboda ɗanɗanonsa da kuma kuzarin da yake bayarwa nan take.
Tun da sinadaran sa na asali shi ne hatsi irin su gero, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin abinci mai gina jiki sosai, akwai fa'idodi da yawa a shan Kunu.
Ga masu fama da ciwon suga, gero yana da amfani saboda yana da ƙarancin ta’azzara sinadarin suga a jini, kuma yana tattare da sinadaran furotin da fiber ba.
A cewar masana abinci, Kunu yana taimakawa wajen narkar da abinci, da kuma inganta lafiyar hanji, musamman idan aka yi shi daga gero ko dawa. Fa'idar sinadaran ƙarfe, calcium, da magnesium wani ƙarin alheri ne.
Daga tsamiyar da ke cikin Kunu, ana samun bitamin B, wanda yake da muhimmanci don kiyaye ruwa a jiki da kuma samar da kuzari.
A al'ada, wasu nau'ikan Kunu ana ganin suna taimakawa wajen ƙara yawan madara ga mata masu shayarwa.
Ana samun Kunu da ake iya haɗawa cikin sauri a fakiti a kasuwannin Nijeriya, wanda ke ɗauke da garin gero, tsamiya, da kayan ƙamshi. Yana da sauƙin haɗawa ta hanyar zuba ruwan zafi a cikin ƙullin da aka haɗa.
Dandanon Ƙasar Hausa
Sinadaran yin Kosai a gargajiya sun haɗa da wake mai ido-baki, wake fari da jan wake, ko nau'in wake na zuma, waɗanda duka suna daga cikin shahararrun wake a Afirka ta Yamma.
Ana jiƙa wake a cikin ruwan ɗumi na tsawon sa'o'i kafin a fitar da bawon. Ana wanke bawon kafin a busar da waken ko kuma a niƙa shi kai-tsaye har sai ya zama laushi sosai.
Akan ƙara kayan miya kamar albasa, tattasai, barkono, ko tafarnuwa a cikin ƙullin. Kuma ana ƙara gishiri da kayan ƙamshi, yayin da wasu ke zuba ɗan manja don gyara launi.
Don samun Kosai mai laushi, ana kaɗa ƙullin a cikin kwano na tsawon mintuna kaɗan. Sannan ana iya saka ƙwai, kifi, nama, da albasa yankakkiya don ƙara masa armashi.
Ana soya Kosai a cikin mai mai zafi, yawanci a cikin kascon suya. Akan yi amfani da cokali mai tsawo ko ludayi don zuba ƙullin ɗaya bayan ɗaya a cikin man mai zafi. Idan gefe ɗaya ya yi launin soyuwa, sai a juya shi don soya ɗayan ɓangaren.
Cikakken abincin
Kosai ya fi kyau a ci shi da zafinsa bayan an tsamo shi daga kasko, wani lokaci a matsayin abin ci na gefe.
Wake da ake amfani da shi wajen yin Kosai yana da sinadaran ƙarfe da folate, yayin da kuma yake ɗaya daga cikin mafi kyawun tushen furotin na tsirrai.
Yayin buɗa-baki, Kosai na da daɗin ɗanɗano a baka, musamman ga wanda ya yini yana azumi. Ba abin mamaki ba ne cewa a yawancin sassan Afirka ta Yamma, buɗa-baki ba ya cika ba tare da ɗan Kosai ba.