Babban mai bai wa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA shawara, wato Arsene Wenger yana neman a yi sauyi a tsarin ƙaramar gasar Turai ta Europa.
Wenger wanda toshon kocin Arsenal ne, yana ganin zai fi dacewa a ce ƙungiyar da ta lashe Europa ba ta samu shiga babbar gasar Zakarun Turai ba kai-tsaye.
Yana ganin zai fi dacewa a ce ƙungiyar da ta ci kofin ta samu damar buga gasar kanta a shekara ta gaba, maimakon hayewa babbar gasar Zakaru.
A halin yanzu ƙungiyoyin Ingila biyu, Manchester United da Tottenham suna dab da kai wa wasan ƙarshe na Europa, wanda bisa doka ɗayansu zai samu zarcewa gasar Zakarun Turai ta baɗi kai-tsaye.
Bayan buga ƙafar farko ta tagwayen wasan dab da na ƙarshe, Man United ta doke Athletic Club da ci 3-0, yayin da Tottenham ta doke Bodo/Glimt da ci 3-1. Wannan ya sa ake ganin duka ƙungiyoyin biyu za su kai wasan ƙarshe kuma ɗaya ta ɗaga kofin.
Me Wenger ya ce?
Da aka tambayi Arsene Wenger game da dacewar kulob ɗin da ya lashe Europa ya samu cancantar shiga Zakarun Turai, Wenger ya faɗa wa beIN Sports cewa, "Ya kamata su cancanci sake buga gasar Europa, ba wai lallai gasar Zakarun Turai ba.”
“Ganin cewa a gasar da ma an samu ƙungiyoyi da dama da suka cancanta buga gasar, ƙungiyoyi biyar (daga Ingila) sun cancanta. Don haka idan ka duba wataƙila ya kamata a yi sauyi.”
A yanzu dai za a zura idon don ganin tsakanin Tottenham da Man U wa zai ba mara ɗa kunya, kasancewar ƙungiyoyin biyu da ƙyar suke iya cin wasa a gasar Firimiya ta Ingila.
Hasali ma, Man U tana mataki na 15 ne a teburin Firimiya, ita kuma Tottenham tana na 16. Wannan ya haifar da tababa kan dacewar a ce kulob ya kasa taɓuka komai a gida, amma ya shiga babbar gasar Turai.
Ranar Alhamis 8 ga Mayu ne ƙungiyoyin biyu za su san matsayinsu a gasar ta Europa, inda ɗaya ko dukansu za su je wasan ƙarshe na gasar, wadda za a buga a birnin Bilbao na Sifaniya.