Ƙaramin Ofishin jakadancin China a Istanbul, tare da ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba na Turkiyya da shugabannin kasuwanci, sun yi bikin ranar ƙawancen Turkiyya da China ta hanyar dasa bishiya 10,000 a Istanbul.
Da yake jawabi a ranar Lahadi, Kwansol Janaral Weir Xiaodong ya ce taron na fito daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin su da kuma aniyar cim ma burin kawar da iskar carbon baki ɗaya nan da 2025 ta hanyar diflomasiyyar muhalli.
Ya kuma ci gaba da cewa ƙasashen sun bayar da muhimmanci sosai ga haɓaka bishiyoyi, in ji Wei: “Ina matuƙar farin cikin ganin haɗin kai a aikace tsakanin ƙasashenmu wanda ya shafi ɓangarori da dama da ayyuka a fannoni daban-daban na haɓaka bishiyoyi da cigaba mai ɗorewa. Ina sauraron ganin haɗin kai mai ƙarfi tsakanin China da Turkiyya ba wai a ɓangaren diflomasiyya kawai ba. Na yi amanna wannan zai amfani kasashenmu biyu da ma duniya.”
Wei ya kuma yi ƙarin haske kan muhimmancin bikin, wanda aka yi a yankin Arnavutkoy da ke kusa da filin jirgin saman Istanbul. “Wajen da muke dasa bishiya a yau na kusa da filin jiragen sama na Istanbul, wanda na da muhimmanci sosai saboda sashen sufurin na amfani da mai sosai, a saboda haka akwai buƙatar mu yi wani abu game da batun.”
Burin kawar da iskar carbon nan da 2050
Mustafa Cifci, mataimakin Kungiyar Masu Habaka Dazuka ta Turkiyya wadda abokiyar yin dashen ce, ya jaddada muhimmancin taimaka wa Turkiyya wajen cim ma manufofinta masu ɗorewa.
“A matsayin ƙungiyarmu ta Turkiyya Koriya, muna ƙarfafa gwiwar dukkan kamfanoni da su shiga ayyukan dasa bishiya a kowacce shekara don taimaka wa a cim ma manufar kawar da iskar carbon nan da 20250,” in ji Ciftci. Ya gode wa Hukumar Yanki Mai Kula da Gandun Daji saboda kawo bishiyun da aka dasa.
Kemal Aygenli, mataimakin shugaban Gundumar Arnavutkoy, ya yi maraba da ayyukan habaka dazukan, inda Ganimet Khasia, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Yankin Hubei na China, ya bayyana fatan cewa za a dinga tuna wa da alakar Turkiyya da China ta hanyar kawance, so da kauna, da kula da muhalli.