Hasan Celebi: Baturken da ya ƙawata Masallacin Manzon Allah da na Sultan Ahmet da aikin zayyanarsa
Hasan Celebi: Baturken da ya ƙawata Masallacin Manzon Allah da na Sultan Ahmet da aikin zayyanarsa
Aikin zayyanar Hasan Celebi ya karaɗe masallatai a faɗin duniya, amma ɗalibansa ne suke tuna nasararsata wajen ci gaba da ɗabbaka ayyukansa na fasahar zayyana.
20 Maris 2025

An fi saninsa da suna “Shugaban Masu Zayyana,” Hasan Celebi, wanda da sa hannunsa a ƙawata masallatai da dama a duniya, ya rasu a Istanbul ranar 24 ga Fabrairu yana da shekaru 88.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Celebi, inda ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da dangi da dalibansa a wani sakon da ya wallafa a X.

Celebi ya sadaukar da rayuwarsa wajen kula da fasahar zayyana na rubutun Musulunci, yana farfado da kuma kiyaye wannan fasaha da ta samo asali daga al’adun Daular Usmaniyya.

Kadan ne suka bayar da gudunmawa ga wannan al’ada kamar yadda Celebi ya yi, wanda ayyukansa ba kawai ƙawata masallatai suka yi ba a duniya, har ma dalibansa suna ci gaba da yaɗa koyarwarsa.

“Babu wani malamin zayyana da ya kai shi wanda ayyukansa suka bayyana a masallatai da yawa haka, kuma ya horar da dalibai da yawa,” in ji Ayten Tiryaki, wata malamar zayyana mai lambar yabo, a hirarta da TRT World.

Ayyukan Celebi ba su tsaya a gidajen adana tarihi ko takardu kawai ba—sun ƙawata bangwayen wasu daga cikin masallatai mafiya daraja a duniya, ciki har da Masallacin Annabi a Madina da Masallacin Sultan Ahmet a Istanbul.

Ana samun ayyukan zayyanarsa a Turkiyya da Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa. Har ila yau, da rubutunsa ne aka ƙawata hubbar Dome of the Rock na Masallacin Ƙudus da Masallacin King Fahd a Los Angeles, da Masallacin Sakirin a Istanbul.

A takaice, sadaukarwarsa ga zayyana ta tabbatar da ɗorewar wannan fasaha. Ta hanyar ɗalibansa, koyarwarsa ta ci gaba da yaɗa wannan fasaha zuwa gaba.

“Dalibansa suna ci gaba da horar da wasu. Saboda haka, fasahar zayyana ta yadu a duniya baki daya kuma tana ci gaba da bunƙasa,” in ji Tiryaki.

An haifi Celebi a Erzurum, Turkiyya, a shekarar 1935, lokacin da fasahohin gargajiya na Daular Usmaniyya ke raguwa. Amma a inda wasu suka fuskanci koma baya, shi ya ga nauyi.

Ba tare da tsoro ba, ya nemi manyan malamai na karshe na al’adun Daular Usmaniyya, inda ya koya daga Hamid Aytac, wanda ya kasance daya daga cikin ‘yan kadan da suka rage na makarantun gargajiya.

“Hasan Celebi ya kasance mai bin gargajiya. Ya sani, ya rubuta, kuma ya koyar da nau’ukan zayyana da yawa.

“Yana da kyakkyawan tunani da ƙarfin hadda da basira sosai. Yakan ba da labarai da tsara baituka, da kuma tarihin rayuwarsa a darussansa.

“Musamman idan ya yi magana kan rayuwarsa da shekarun ƙuruciyarsa, sha’awarmu gare shi tana ƙaruwa,” in ji Tiryaki, ɗaya daga cikin ɗalibansa.

Kwarewa a rubutun zayyanar masallatai

An horar da Celebi a matsayin mai bin al’adun gargajiya, amma ya ƙware sosai a rubutun Jali Thuluth da Jali Diwani—wanda aka san su da salo na musamman.

Dalibinsa daga Siriya, Muhammed Enes Huri (Sami), ya bayyana tasirin malaminsa kan rubutun masallatai: “Makarantar kira’a tana ci gaba daga al’adun Daular Usmaniyya. Malam Hasan ya samu tasiri sosai daga Hamid Aytac.

Celebi ya kasance ƙwararre a mafi yawan rubutun zayyana, musamman Jali Thuluth da Jali Diwani, amma ya fi fice a rubutun masallatai.”

Rubutun Celebi yana bayyana girma da sauki, yana haɗe da kyawawan zane-zanen gine-ginen Musulunci.

“Saboda ƙwarewarsa a cikin tsarin da aka hade, an nemi shi don tsara zayyanar masallatai da yawa a ciki da wajen Turkiyya,” in ji Huri.

Abin da ya bambanta Celebi ba kawai fasaharsa ba ce, amma ikon da yake da shi na daidaita rubutu da gine-gine. Rubutunsa ba kawai ado ne mai tsayi ba; suna zama wani bangare mai muhimmanci na wuraren da suka ƙawata, kamar dai dama zanen ya kasance a bangon ne tun fil azal.

Celebi ya samu kwangila don rubutun zayyana ga OIC a Jeddah, kuma ya gyara rubutun Masallacin Manzon Allah SAW a Madina.

Celebi ya gudanar da baje-kolinsa na farko a IRCICA a 1982, sannan ya yi a Malaysia da Jordan.

A 1987, ya shafe shekara guda yana rubutun zayyanar Masallacin Quba da aka sake ginawa a Saudiyya, daga baya ya gudanar da taruka da baje-koli a Kuala Lumpur a 1992.

A 1994, ya yi bikin cika shekaru 30 a fannin zayyana tare da baje-koli na musamman. Tun daga 1976, ya horar da kusan dalibai 100 a duniya, yana tabbatar da gado mai ɗorewa a matsayin daya daga cikin malamai mafi tasiri a fannin zayyana.

Celebi ya samu lambar yabo ta Necip Fazil da kuma Kyautar Shugaban Kasa na Turkiyya don Al’adu da Fasaha.

“Ku zo idan kuna da haƙuri sosai”

Sunan fitaccen mai zayyanar ya kasance a rubuce ba kawai a tarihi ba, har ma a cikin gine-ginen ibada. Dalibansa suna rubutu, kuma ta hanyar su, Celebi har yanzu kamar yana riƙe alkalami ne.

Ba kawai samar da rubutun zayyana Celebi ya yi ba, har ma ya horar da sabbin ɗalibai da suka zama malamai a fannin, yana tabbatar da ɗorewar wannan fasaha.

“Na fara karatun a 1983 kuma na samu lasisi a 1989,” in ji Tiryaki. “Yakan ce wa wadanda suke son fara darussa tare da shi, ‘Ku zo idan kuna da haƙuri sosai.’”

Haƙurinsa da kirkinsa sun bar wani abu mai zurfi a zuƙatan dalibansa. Bai taba karaya ba, ko kuma ya yi watsi da dalibi mai ba shi wahala.

Maimakon haka, ya jagorance su da hikima, yana ba da gyara mai kyau da kuma ƙarfafa gwiwa.

Dalibinsa daga Afirka ta Kudu, Muhammed Hobe, ya ce: “Karatu tare da Malam Hasan albarka ce. Ya kasance mai hakuri sosai da dalibai, mai kirki sosai.

Bai taba sukar dalibi da tsauri ba. Yakan nemi mafi kyawun haruffa kuma ya yi sharhi a kansu. Yakan ce mu mai da hankali kan tsarin haruffa kafin wani abu.”

Celebi ya samu ƙwarewa a fannin zayyana ta hanyar jajircewa.

“Yakan ce don samun nasara a fannin ƙira’a, mutum ya kamata ya yi aiki na awanni 30,” in ji Tiryaki.

Alkalamin da ba zai taɓa bushewa ba

Tasirin Hasan Celebi a duniyar zayyana ta Musulunci ba zai misaltu ba. Dalibansa sun zama malamai a karan-kansu, suna yada koyarwarsa a nahiyoyi daban-daban.

Amma abin da suka fi tunawa da shi ba kawai fasaha ba ce, har ma da tawali’unsa da kuma yadda ya ba da kansa wajen koyarwa.

“Abin da ya fi burge ni shi ne yadda ya taimaka wa dalibai da tawali’u. Ya kasance malami na gaskiya. Abin da ya fi sa ni farin ciki shi ne yadda ya ba ni aikin koyar da dalibai. Wannan ya taɓa zuciyata sosai,” in ji Huri.

Kyautarsa ta wuce aji. Dalibansa ba kawai dalibai ba ne; suna kama da iyalinsa.

“Ya ba ni shawara a gidansa kan yin aure da matar da na aura,” in ji Hobe. “Shi ne ya nemi izinin auren kuma ya gudanar da bikinmu.

Daga baya ya ba da shawarar sunan da za a sa wa ‘yata. ‘Yata ta yi sa’a ta hadu da malam sau da yawa kuma tana kiransa ‘Dede’ (kaka). Ya bar babban giɓi a zuƙatanmu, kuma za a yi kewarsa har abada.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us