Wata kotun soji a Nijeriya ta yanka wa wani soja mai muƙamin kurtu, Adamu Mohammed, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kashe budurwarsa.
Kwamandan batalita ta 82 ta rundunar sojin Nijeriya Manjo-Janar Oluyemi Olatoye, ne ya ƙaddamar da kotun sojin mai alƙalai 11 a watan Fabrairu shekarar 2025 domin hukunta sojoji masu laifi a rundunar.
Wata sanarwa da muƙaddashin mataimakin mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Jonah Unuakhalu ya fitar ta ce kotun ta samu jagorancin Birgediya Janar Sadisu Buhari.
“Shugaban kotun, Birgediya Janar Sadisu Buhari, a lokacin da yake yanke hukunci kan wanda ake tuhuma, Adamu Mohammed, ya bayyan cewa an same shi da laifin kashe budurwarsa, Hauwa Ali, laifin da ake iya hukuntawa a ƙarƙashin sashi na 106 (a) na dokar sojin Nijeriya ta shekarar 2004,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa alƙalan kotun dukka sun sami sojin da laifi ne bayan sun yi nazari kan hujjojin da aka gabatar a gabansu da bayanan tarihin aikin sojan tare da la’akari da afuwar da wanda ake tuhuma da lauyansa suka nema.
Sai dai kuma kotun ta ce dole a aiwatar da hukunci mafi tsauri domin yi wa wadda aka kashen adalci da kuma tabbatar da doka da oda.
“Saboda haka, kotun sojin ta yanke hukuncin cewa sojan da ake tuhuma [mai lamba] 21NA/80/6365 Adamu Mohammed, za a kashe shi ta hanyar rataya saboda laifin kisa " in ji Birgediya-Janar Sadisu.
Kazalika, kotun sojin ta yanke wa wani soja mai muƙamin kurtu, Abubakar Yusuf, hukuncin ɗaurin shekaru shekara goma a gidan yari bayan an same shi da laifin fashi a wani shago a Enugu.
Sanarwar ta ce rundunar sojin Nijeriya tana jaddada wa ‘yan ƙasar cewa za ta ci gaba da dagewa wajen tabbatar da ɗa’a game sa yadda take gudanar da ayyukanta.