An fayyace wakilan da za su ci gaba da tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine a Istanbul.
Ministan Harkokin Waje na Turkiyya, Hakan Fidan da wakilan gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Sakataren Harkokin Waje, Marco Rubio, da tawagar Ukraine ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro Rustem Umerov, da wakilan Rasha mai jagorancin Mashawarcin Shugaba Putin, Vladimir Medinsky za su shiga tattaunawar.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy ya zartar da dokar kafa kwamitin wakilan a hukumance, don su shiga tattaunawa zaman lafiyar.
Wakilan Ukraine suna ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro Rustem Umerov, kuma an shirya za su haɗu da jami’an Turkiyya, Rasha, da na Amurka.
Haka nan tawagar za ta ƙunshi Mataimakin Ministan Harkokin Waje, Sergiy Kyslytsya, da Mataimakin Shugaban Hukumar Tsaro ta (SBU), Oleksandr Poklad, da Mataimakin Shugaban Hukumar Leƙen Asiri, Oleh Luhovskyi, da Mataimakin Shugaban Soji, Oleksii Shevchenko, da Mataimakin Shugaban Babbar Cibiyar Leƙen Asiri (GUR), ta Ma’aikatar Tsaro, Vadym Skibitskyi, da Mataimakin Shugaban Hedikwatar Sojin Sama, Yevhenii Shynkarev, da Mataimakin Shugaban Hedokwatar Sojin Ruwa, Oleksandr Dyakov, da Shugaban Sashen Dokokin Ƙasashen Waje, Oleksii Malovatskyi, da Babban Jami’in Gudanarwa na Hukumar Aikace-aikace, Oleksandr Sherikhov, da Jami’in Tsare-tsare da Tallafawa na Babban Kwamanda Rundunonin Soji, Heorhii Kuzmychev, da Mashawarcin Shugaban Fadar Shugaban Ƙasa, Oleksandr Bevz.
Tawagar Rasha da ke ƙarƙashin Vladimir Medinsky, za ta ƙunshi Mataimakin Ministan Harkokin Waje, Mikhail Galuzin, Babban Jami’in Babbar Cibiyar Leƙen Asiri ta Rasha (GRU), da Darakta Igor Kostyukov, da Mataimakin Ministan Tsaro na Rasha, Aleksandr Fomin.
Sauran jerin ƙwararru a tawagar sun haɗa da Mataimakin Babban Daraktan Sashen Yaɗa Labarai na Rasha, Aleksandr Zorin da Mataimakin Daraktan Sashen Tsarin Ƙasa na Shugaban Rasha a Ɓangaren Jin-ƙai, Yevgeniya Podobreyevskaya, da kuma Daraktan Sashe na Biyu na Gamayyar Ƙasashe Masu Zaman-kansu a Yankin Rasha, da ke Ma’aikatar Harkokin Waje, Aleksandr Polishchyuk da Mataimakin Daraktan Babbar Cibiyar Haɗn-kan Soji ta Ƙasa-da-Ƙasa da ke Ma’aikatar Tsaro, Vladimir Shevtsov.