Ministan Kudi da Baitulmali na Turkiyya Mehmet Simsek ya gana da Sakataren Baitulmali na Amurka Scott Besent a Washington a ranar Laraba don tattauna yadda za su faɗaɗa alaƙa kan tattalin arziki da dabarun ayyuka tare a yankunansu, in ji Ma’aikatar Kudi ta Turkiyya.
Gwamnan Babban Bankin Turkiyya Fatirh Karahan ma ya halarci ganawar inda ya halarci zaman da masana suka kira “Yanayin Kawo Cigaba”.
Dukkan ɓangarorin biyu sun sake tabbatar da aniyar Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Shugaba Donald Trump ta haɓaka alaƙar ƙasashen biyu ƙawaye a NATO.
Mayar da hankali ga kasuwanci, zuba jari da makamashi
Tattaunawar ta mayar da hankali kan haɓaka alaƙa a ɓangarori irin su zuba jari, kasuwanci, sufuri da makamashi. Simsek ya bayyana muhimmancin janye wasu ‘yan takunkumai da ke hana tafiyar da haɗin kai a ɓangaren tsaro - ɓangare mai muhimmanci a alaƙar ƙasashen.
Tawagar Turkiyya ta kuma gabatar da ci gaban daidaituwar tattalin arziki da Turkiyya ke samu.
Minista Simsek ya bayyana ƙudurin Ankara na “ɗabbaka buɗaɗɗun manufofin tattalin arziki masu ɗorewa” kamar yadda aka bayyana a baya bayan nan a wasu tarukan ƙasa da ƙasa, ciki har da Gawanar Bazara ta IMF-Bankin Duniya
Baya ga tattalin arziki, ɓangarorin biyu sun kuma tattauna batutun yankunansu.
Jami’an turkiyya sun jaddada buƙatar janye takunkumai kan Siriya inda suka kuma jero kokarin diflomasiyya da Turkiyya ke yi wajen ganin an tsagaita wuta a Ukraine.
Manufar cim-ma burin kasuwancin dala biliyan 100
Tattaunawar ta zo a daidai lokacin da alaƙar tattalin arzikin Amurka da Turkiyya ke haɓaka, inda dukkan gwamnatocin biyu ke da aniyar habaka kasuwancinsu ya kai na dala biliyan 100.
Masu nazari na sa ran za a samu karin tattaunawar kwararru a watanni masu zuwa don habaga tattaunawar da aka yi a yayin ziyarar ta Washington.
A yayin da Turkiyya ke ci gaba da saisaita kanta a matsayin babbar mai taka rawa a sha’anin tattalin arzikin yanki, habaka alaka da Washington zai zama mai muhimmanci.