NIJERIYA
1 minti karatu
Gobara ta lalata rumbun makamai na 'Giwa Barracks' da ke Maiduguri a Nijeriya
Wata sanarwa da rundunar sojojin Nijeriya ta fitar ranar Laraba da maraice ta ce tsananin zafi ne ya haddasa gobara a rumbun makamai da ke Giwa Barracks a Maiduguri da ke Jihar Borno.
Gobara ta lalata rumbun makamai na 'Giwa Barracks' da ke Maiduguri a Nijeriya
Gobarar ta tashi ne a yayin da Jihar ta Borno ke ƙara fuskantar sabbin hare-hare na mayaƙan Boko Haram / Others
1 Mayu 2025

Rundunar sojojin Nijeriya ta tabbatar da ɓarkewar gobara a rumbun makamai da ke barikin sojoji na Giwa Barracks da ke birnin Maiduguri a Jihar Borno ta arewa maso gabashin ƙasar.

Wata sanarwa da Reuben Kovangiya, muƙaddashin mataimakin mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai, ya fitar ranar Laraba da maraice ta ce lamarin ya faru ne “a ɗaya daga cikin wuraren ajiyar makamanmu da ke Giwa Barracks.”

Ta ƙara da cewa “gobarar ta tashi ne sakamakon tsananin zafi da ake fama da shi a Maiduguri.”

Sai dai sanarwar ta ce an shawo kan gobarar sakamakon “ƙoƙari na haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno da kuma wasu motocin kashe gobara daga sauran hukumomin tsaro.”

Reuben Kovangiya ya shaida wa jama’a su yi watsi da rahotannin da ke cewa an kai sabbin hare-hare a birnin na Maiduguri da kewayensa.

Ya ce an tura dakarun rundunar Operation Hadin Kai lungu da saƙo na birnin domin hana ɓata-gari yin amfani da wannan dama wurin yin sace-sace da sauran ayyuka marasa kyau.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us