Idanuwan kananan yaran na bayyana komai ƙarara: ba komai a ciki; cikin bakaken ƙwayoyin idanuwa cike da rashin tabbas.
Akwai wasu karin alamun ma - manyan kawunansu da suka yi wa gangar jikinsu girma, siraran damatsa da kafafuwa. Wadannan alamu ne da ke tabbatar da matsananciyar yunwa.
Sansanin ‘yan gudun hijira na Cox’s Bazar da ke kudancin Bangaladash - wajen da ke dauke da adadin masu neman mafaka mafi yawa a duniya - wadannan alamu ne masu karya zuciya sosai.
Sama da masu neman mafakar Rohingya miliyan guda ne ke zaune a sansanoni 33 a Ukhiya da Teknaf.
Daga ciki akwai yara kanana kimanin 320,000 da ke fama da karancin cimaka. Wannan adadi na ƙaruwa da 22,000 a kowacce shekara, inda ake haifar sabbin jarirai a duniyar da ba za ta iya ci da su ba.
Wadannan masu neman mafakar sun guje wa kisan kiyashi da zalunci a Myammar, amma a yanzu suna fuskantar wani nau’in zaluncin - jan kafa, hana su abinci kullum, gaza kula da lafiyarsu da tsare mutuncinsu.
Kudade na raguwa rikici na ta’azzara
Har zuwa baya bayan nan, Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta dinga baiwa masu neman mafakar dala 12.5 ga duk mutum guda a kowanne wata - wato cent 41 kowacce rana.
Wannan adadi ba zai ishi iyali ba tare da yi musu maganin yunwa. A farkon watan Maris, WFP sun yi gargadi cewa idan ba a kawo agajin gaggawa ba, wannan adadin kudade zai koma dala 6 - wato cent 19 kawai a kowacce rana.
Sai dai kuma, kwanakin baya sun sake duba adadin zuwa dala 12 a wata, ko cent 39 a rana, amma adadin na da hatsari matuka.
Idan za a yi warwara kan wannan adadi da yadda za a kashe shi a Bangaladash, kilo 1 na shinkafa kusan cent 49 ne, waken lentil kuma kilo 1 ana sayar da shi cent 32, inda kaza kilo 1 ake sayar da ita kan dala 2.46.
Abu ne da za a iya gani cikin sauki, sabod ahaka ta yaya iyali mai mutane hudu, da ke karbar dala 1.56 a rana, za su iya cin abincin da zai ishe su.
Wannan ba wai sauyin tattalin arziki ba ne - rushewar ayyukan jin kai ne.
Likitoci na bayyana cewa yaran da ke da shekaru tsakanin daua zuwa uku na bukatar a kalla sinadarin kalori 1,400 kowace rana.
Wadanda ke da shekaru tsakanin tara da 13 kuma na bukatar 1,600, mata manya na bukatar har zuwa 2,400, maza manya kuma na bukatar akalla 2,300, ya danganta da tsayi da girman jikin mutum.
Kudaden taimamon da ake bayarwa a yanzu na barin ‘yan Rohingya a yanayin kasa da yadda ya kamata a ce ana ba su.
Ba nan da nan za a ga illar hakan ba - a lokaci mai tsayi za a gani. Yaran da ba sa samun isasshiyar cimaka na fuskantar gaza girma, garkuwar jiki mai rauni, da dawwamammen cikas din habakar jiki.
Wannan ba ibtila’i ne da ya afku ba zata ba. Musiba ce da ke afkuwa sannu a hankali, a cikin shekaru.
Tun bayan babbar hijirar 2017 ‘yan Rohingya suka shiga tsaka mai wuya da rayuwa marar dadi a Bangaladash, inda sama da mutum 750,000 suka tsere daga yankunansu, abinda MDD ta bayyana a matsayin “babban misalin karar da wata kabila” da sojojin Myammar ke aikatawa.
Hakan ya biyo bayan shekar da dama da ‘yan Rohingya suka dauka suna guduwa Bangaladash, tun farkon 1990, don kaucewa zaluncin da ake ta yi musu.
Amma hankalin duniya - har da ma na masu bayar da taimakon kudade - ya ragu sosai.
A lokacin da na yi magana da wakilan Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), sun bayyana yadda ake samun janyewar taimakon jin kai a kusan shekaru goma da suka gabata.
Lamarin Bangaladash a yanzu ya zama “rikicin jin kai mai dorewa,” ba ya samun kulawar gaggawa ta duniya.
Ma’aikatan taimako sun bayyana yadda hankulan kafafen yada labarai da smaar da kudade suke da alaka da juna - a lokacin da kanun labaran suka bata, haka ma kudaden sun bace an daina ganin su.
WFP na cewa gibin kudaden samar da abinci ya samu ne sabo karancin kudaden tallafi, ba wai saboda matakin da SHugaban Kasar Amurka Donald Trump ya dauka na katse tallafi ga kasashen waje ba.
Amma ragi tallafin da USAID ke bayarwa da kashi 8.8 kan sansanonin ba iya samar da abinci kadai ya shafa ba, har da muhimman ayyuka irin su lafiyae haihuwa, kare cusgunwa mata, da kula da mata masu juna biyu.
A lokacin da na ziyarci sansanonin Kutupalong da Balukhali a watan Maris, na shaida illar da wannan matakin da duniya ta duaka yake janyo wa.
Asibitoci biyar na Kungiyar Kasa da Kasa ta IRC sun daina kula kowa sai idan ana cikin halin gaggawa.
Ma’aikatan sun ce katse kudaden na nufin dole a dakatar da ayyuka zuwa duba mutane da lafiyarsu wanda ke taimaka wa mata da yara kanana da a yanzu suke cikin hatsari.
Mumunar makoma
Akwai matukar damuwa idan aka kalli illa da tasirin dakatar da kudaden nan. Kwararrun da na zanta da su, ciki har da masu kula da sansanonin masu neman mafaka da ma’aikatan Kungiyoyi Masu Zaman Kansu, sun yi gargadi kan yiwuwar fada wa halin dugunzuma.
Sun bayyana yadda yunwa da talauci ka iya jefa jama’a su fada aikata munanan ayyuka, saboda akwai su kula da rayuwarsu.
Wasu sun bayyana daduwar rikici a tsakanin iyali da rahotannin safarar dan’adam.
Tare da sama da mutane miliyan guda da ba su da kasa kuma suke zaune a waje guda - ba sa samun damar samun ayyuka, yin tafiya, ko su shiga cikin al’umar Bangaladash su narke - matsin lambar ya yi yawa.
A yayin da ‘yan Rohingya da dama ke kara tururuwa zuwa kasar, suna guje wa azabar da suke fuskanta a Myammar, to lamarin kara ta’azzara kawai yake.
A baya bayan nan Hukumar Tarayyar Turai ta yi alkawarin bayar da taimakon dala miliyan 79.4 ga jama’ar Rohingya da wasu da rikici ya tsugunar a Myammar.
A wajen WFP, cikin gaggawa ana bukatar dala miliyan 96 don bayar da abinci nan da karshen shekara.
Yanayin bukatar taimakon na da girma sosai. Kuma biris din da aka yi da su ma ya fi girma.
Abinda ke faruwa a Cox’s Bazar ba wai yanayin gaggawar jin kai ba ne - gazawar halayyar dan adam ce da rashin cika alkawari.
‘Yan Rohingya sun fuskanci mummunan yanayin da za a iya hakaito shi ba, ciki har da kisa da azabatarwa, fyade, kona gidajensu, da raba su da kasarsu.
Kuma yanzu muna kallon yunwa na addabar su, ba saboda yaki ba, saboda rashin tausayin duniya.
A lokacin da duniya ta fara shaida wahalar da suke ciki, an nuna tausayi da taimako daga kowane bangare.
Amma tausayi na da ranar gushewa a fagen labaran kasa da kasa. Bayar da kudade na bisa sharadin mayar da hankali. Kamar yadda muke gani, mayar da hankalin na gushewa.
‘Yan Rohingya na cikin tarko - a sansanoni, a tarihi, a cikin ala kakai. Har yanzu suna nan, suna ta shan wahalar. Duniya ta taimaka kar ta juya musu baya.