NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan rundunar soji bayan ƙaruwar hare-haren Boko Haram
Rundunar sojin ba ta alaƙanta sabon naɗin da ta yi kan ƙaruwar hare-haren da ake samu a arewa maso gabashin ƙasar ba.
Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan rundunar soji bayan ƙaruwar hare-haren Boko Haram
Rundunar sojin ƙasar dai ba ta alaƙanta naɗin da ta yi wa Janar Abubakar da ƙarin hare-haren 'yan ta'adda ba / Nigerian army
5 awanni baya

Hukumar sojin Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci yaƙin da take yi da ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin ƙasar.

Wannan na zuwa ne bayan ƙaruwar hare-haren ‘yan Boko Haram a yankin, cikin watanni huɗun da suka gabata. Hare-haren sun kashe fararen-hula da sojoji da dama.

Sabon kwamandan da aka naɗa shi ne Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar, wanda shi ne kwamanda na 15 a yaƙin da Nijeriya ke yi da ‘yan Boko Haram, da ISWAP a arewa maso gabashin ƙasar.

Wata sanarwa daga runduna ta musamman da aka yi wa laƙabi da ‘Operation Hadin Kai’ ita ta tabbatar da wannan sauyi.

Sanarwar da muƙaddashin mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Reuben Kovangiya ya sanya wa hannu, ta ce a baya Janar Abubakar ya riƙe muƙamin mataimakin kwamandan kwalejin tsaron Nijeriya, da kuma kwamandan wani muhimmin shiri a arewa maso tsakiyar Nijeriya.

Ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP sun zafafa kai hare-hare a arewa maso gabashin Nijeriya cikin ‘yan makonnin nan.

Waɗannan hare-haren sun ƙara fargabar dawowar hare-haren masu iƙirarin jahadi, inda a halin yanzu salon hare-haren ya ƙunshi amfani da jirgi mara matuƙi ɗauke da makamai da kuma bama-bamai da suke ɗanawa kan muhimman hanyoyi, in ji masana harkokin tsaro.

A ranar Talata, ISWAP ta ɗau alhakin kai wani hari a jihar Borno, wanda ya kashe aƙalla mutum 26, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a wata sanarwar da ta fitar a shafin Telegram.

Masu ta da ƙayar bayan sun shafe shekara 15 suna yaƙar dakarun tsaro a arewa maso gabashin Nijeriya, kuma suna yawan amfani da bama-bamai da suke haɗawa wajen kai hare-hare kan fararen hula da dakarun tsaro.

Rundunar sojin Nijeriya ba ta alaƙanta sabon naɗin da ta yi da ƙarin hare-haren da ake samu ba a yanzu ba.

"Abin taƙaici ne cewa Boko Haram na ƙara yawan hare-hare da garkuwa da mutane a cikin garuruwa da dama, kusan kullum ba tare da cewa an ƙalubalance ta ba, lamarin da ya nuna cewa jihar Borno na rasa iko," kamar yadda gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana wa shugabannin dakarun tsaro cikin wannan watan.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us