DUNIYA
1 minti karatu
Kasashe sun yi alkawarin $170 ga WHO gabanin ficewar Amurka
China da Qatar da Switzerland da wasu kasashen sun yi alkawarin dala miliyan 170 ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Kasashe sun yi alkawarin $170 ga WHO gabanin ficewar Amurka
Kasashe da dama sun yi alkawarin gomman miliyoyin daloli ga WHO bayan Amurka ta sanar da cewa za ta daina bai wa hukumar ta lafiya ta duniya agaji. / Reuters
21 Mayu 2025

Ƙasashen China da Qatar da Switzerland da sauransu sun yi alƙawarin bayar da sama da dala miliyan 170 ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a taronta na ranar Talata.

Har ila yau, ƙasashen sun amince da ƙarin kuɗaɗen don taimakawa wajen rage giɓin da ake sa ran za a samu na babbar mai bayar da agajin, Amurka.

“Ina godiya ga kowace ƙasa mamba da abokan hulɗar da suka yi alƙawarin bayar da agaji,” in ji Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban daraktan hukumar ta WHO a cikin wata sanarwa.

Ya ƙara da cewa: "A cikin yanayi mai wahala ga lafiyar duniya, waɗannan kuɗaɗe za su taimaka mana wajen adanawa da kuma faɗaɗa ayyukanmu na ceton rai."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us