Enkipaata: Bikin balagar yara maza a ƙabilar Maasai
Enkipaata: Bikin balagar yara maza a ƙabilar Maasai
Fiye da yara 900 ne daga ƙabilar Maasai waɗanda ke zaune tsakanin iyakar Kenya da Tanzania ke karɓar horo na musamman, domin koyon ɗabi’un da suka dace a daidai lokacin da girma ya zo musu.
2 Mayu 2025

Ɗaruruwan jama'a daga al'ummar Maasai da masu sha'awar su ne suka hallara a garuruwa daban-daban da ke kan iyakar Kenya da Tanzaniya don shaida Enkipaata mai ɗimbin tarihi.

Al'ada ce ta musamman ga "mutanen kan tsauni", kamar yadda aka kuma san Maasai, yayin da suke haɗuwa cikin tufafinsu na ado masu launi, adon fuska, duwatsun ado na wuya da sarƙoƙi.

Kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe sun yi ta tashi a cikin dazuka da ake gudanar da waɗannan bukukuwa, babu wanda ya damu da batun layin da Turawan mulkin mallaka suka shata domin raba kansu.

Al’adar mafari ce ta abu uku, inda maza a al’adance za su tashi daga ƙananan maza zuwa balagaggu, kuma da haka za su iya ayyukan da balagaggu ke yi kamar aure da kuma kula da al’umma.

Ilimi da al’ada

A al’adance, wannan bikin wanda ake gudanarwa duk bayan shekara 10 ko kuma fiye da haka, yana haɗa maza waɗanda ke tsakanin shekara 15 zuwa 30 kuma ana shafe shekara ana gudanar da shi, sai dai tuni bikin ya sauya zuwa wata ɗaya domin tafiya daidai da kalandar karatu ta yaran ɗalibai, haka kuma a yanzu babu mai kashe zaki a wurin bikin kamar yadda ake yi a baya.

Ɗan Joyce Naingisa zaiu shiga wannan bikin na Enkipaata, kuma ko da yake tana da shekara 34, wannan al’ada ta sauya sosai a rayuwarta.

Ta ce: “Mijina ya daina makaranta na tsawon shekara guda don ya halarci makaranta.

"Amma yanzu su ne shugabanni, kuma sun san muhimmancin ilimi, don haka yaran nan za su bi wannan al’adar, amma duk da haka muna tabbatar da sun je makaranta."

Ta hanyar ilimantar da matasa game da rawar da za su taka a nan gaba a cikin al'ummar Maasai, bukukuwan suna taimaka musu su fara koya musu tarbiyya, sannan a matsayinsu na dattawan matasa, kuma a ƙarshe a matsayin manyan dattawa.

Girmamawa da ɗaukar nauyi, kiyaye zuriya, mika mulki daga wani zamani da aka saita zuwa na gaba da bayar da ilimin al’adu na dauri, kamar dangane da kiwon dabbobi, magance rikice-rikice, almara, al'adu da basirar rayuwa, wasu daga cikin muhimman daɓi'u ne da aka sanya a cikin waɗannan al’adu.

Sai dai kamar sauran jama'a a fadin Afirka, wannan al'ada tana fuskantar barazana ta hanyar zamanantar da al'umma, sauyin yanayi da kuma raguwar filayen da suke zama saboda faɗaɗar birane.

Saboda haka, hukumar UNESCO ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana al’adar Enkipaata a matsayin wadda ya kamata a ci gaba da ɗabbaƙawa, amma da wasu sauye-sauye da za su tafi da zamani.

Isaac Mpusia, ɗan shekara 16 da ke makarantar sakandare, wasu yara maza sun kai masa ziyara a gida inda suka buƙaci ya shiga bikin.

“Idan ka zo nan, za ka koyi abubuwa da yawa da iyayenmu suka yi,” in ji Mpusia. “Dole ka kasance mai ɗa’a.”

A bana, yara 900 ne aka bai wa horo sosai, daga ciki har da horo kan kula da iyali, aure.

Kuma bayan kammalawa, ana sanya wa kungiyar suna na musamman Ileratu, wanda ke danganta su a matsayin ‘yan uwan ​​juna har karshen rayuwarsu.

Isaac Mpusia ya ce: “Idan muka hadu nan gaba, za mu san juna. "Saboda mun fito daga rukuni guda."

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us