Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana aniyar Turkiyya ta zurfafa alaƙa da Italiya a ɓangarorin kasuwanci, da tsaro, da diflomasiyya, bayan wata babbar ziyara da ya kai Rome inda ƙasashen biyu suka gudanar da taron gwamnatoci karo na huɗu.
Da yake tattaunawa da ‘yan jaridu a cikin jirgin sama yayin komawa gida, Erdogan ya bayyana tafiyar a matsayin mai nasara da alfanu, yana mai karin haske kan yiwuwar aiki tare a Afirka, musamman a ɓangarorin tsaro da taimakon jin ƙai.
Ya haɗa gwiwa wajen jagorantar taron da Firaministar Italiya Giorgia Meloni tare da jaddada cewa gwamnatocin biyu sun amince da ɗaga martabar alaƙarsu ta kasuwanci daga dala biliyan 30 zuwa dala biliyan 40 a nan gaba kaɗan.
“Tun baya ma alaƙarmu da Italiya na kan kyakkyawar turba. Alaƙarmu ta tarihi, da amfani da teku guda, da haɗin kai mai zurfi, da buƙatu iri guda, da batutuwa da dama da muke da ra’ayi guda a kan su, duk na ƙarfafa gwiwowinmu wajen bunƙasa alaƙar. Shi ya sa muke da manufofi masu kyau da muke da burin cim ma wa.
Ya ƙara da cewa a yayin ziyarar an sanya hannu kan yarjeniyoyi 11.
Haɗin Kan Samar da Tsaro
Ɗaya daga cikin manyan ɓangarori da suke samun nuna sha’awa shi ne tsaro. Erdogan ya yi nuni ga karuwan hadin kai tsakanin masana’antun tsaron Turkiyya da takwarorinsu na Italiya, musamman yarjejeniyar baya bayan da aka kulla tsakanin masu samar da jiragen yaki marasa matuka a Turkiyya Baykar da kamfanin kayan tsaro na Italiya Leornado.
Ya ce kofofin Turkiyya a bude suke don hadin kai a bangarorin tsaro, sufurin jiragen sama, da fannonin fashahar kere-kere, yana mai cewa ƙwarewar Italiya da karfin samar da kayayyaki na Turkiyya na iya zama mai amfani a gare su.
Da yake amsa tambayoyi game da rikicin yankuna da kokarin da kasashe suke yi, irin su Girka, wajen hana Turkiyya kulla alakar tsaro, Erdogan y ace Turkiyya ta mayar da hankali ga samar da isassun kayan tsaro ta yadda za ta dogara da kanta.
Ya kuma jaddada cewa za a ci gaba da neman kulla kyakkyawar alakar makotaka ta hanyar diflomasiyya da makociyarsu Girka.
Da yake tabo batun cigaba a Afirka, Erdogan ya marabci shawarar da Italiya ta kawo na hada gwiwa a yi aiki a nahiyar, ana hada wa da manufar Turkiyya ta ‘win-win’ (cude ni in cude ka) a Afirka ta hanyar kasuwanci, zuba jari da kokarin jin kai.
“Ba mu ga wani dalili ba na ba za mu tafi tare da Italiya ba a Afirka. Wannan hadin kai ne da a shirye muke mu yi shi,” in ji shi.
Erdogan ya kuma tabo yakin da ake ci gaba da yi da ‘yan ta’addanci, a yayin da ake yada jita-jitar cewa kungiyar PKK na iya sanar da ajje makamai nan da wani dan lokaci. Ya ce Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya na bi diddigi da sanya oidanu kan lamarin tare da ci gaba da kokarin kawar da ta’addanci baki daya.
“Mun dukufa wajen ganin mun barwa al’umma mai zuwa Turkiyya da babu ‘yan ta’adda a cikn ta,” in ji shi.
Game da batun Syria, Erdogan ya sake tabbatar da matsayar turkiyya ta kare nmartabar iyakokin makociyarta ta bangaren kudu.
Ya yi watsi da yunkurin baya bayan nan na reshen PKK/YPG na kafa tsarin tarayya a arewacin Syria, inda ya kira hakan da ba abu ne mai yiwuwa ba.
“Ba za mu bayar da aikata ba daidai ba a yankinmu, kuma ba za mu bayar da dama a aikata duk wani abu da zai tayar da hankali a aSyria ko yankin ba.”
“Jami’an gwamnatin Syria sun bayyana cewa babu wata hukuma idan ba gwamnatin Syria ba, kumababu wata kungiya mai dauke da makamai sai sojojin Syria, da za a amince da ita a Syria.” Ya fada.
Shugaban ya kuma yi tsokaci da cewa ya aike da sakon gayyata zuwa Turkiyya ga Shugaba Sergio Mattarella da Firaminista Meloni.
Ya jaddada tsammanin Ankara na samun babban goyon baya daga Italiya don shiga Tarayyar Turai, inda ya bayyana muhimmancin tattalin arziki da Turkiyya ke da shi a Turai da ma sha’anin tsaro.