SIYASA
2 minti karatu
Kotu a Finland ta tuhumi dan awaren Baifra ta Nijeriya Simon Ekpa da laifin ta’addanci
Tuhume-tuhumen da aka yi wa Simon Ekpa na da alaƙa da ƙoƙarin da yake yi na kafa ƙasar Biafra a Nijeriya, in ji Hukumar da ke Gabatar da Kara ta Finland.
Kotu a Finland ta tuhumi dan awaren Baifra ta Nijeriya Simon Ekpa da laifin ta’addanci
Simon Ekpa na da shaidar zama dan kasashen Finland da Nijeriya. Photo / Simon Ekpa / X / Others
15 awanni baya

Masu gabatar da kara na Finland a ranar Juma’a sun ce sun tuhumi wani mutum da laifukan ingiza ta’addanci ta yanar gizo, wanda kafafan yaɗa labarai suka bayyana sunansa da ɗan Nijeriya ɗan aware, Simon Ekpa.

Hukumar da ke Gabatar da Ƙara ta Finland ta bayyana cewa ta tuhumi “wani ɗan Finland da laifin da ya shafi zuga mutane su aikata muggan laifuka da manufar ta’addanci da ma shiga ayyukan ‘yan ta’adda.”

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ƙara da cewa an aikata laifukan a garin Lahti a shekarun 2021 da 2024, kuma suna da alaƙa da ƙoƙarin kafa ƙasa mai cin gashin kanta a yankin Biafra na Nijeriya.

Hukumar gabatar da karar ta Finland ba ta bayyana sunan mutumin ba, amma tashar sadarwa ta Finland ta bayyana shi da ɗan aware, Simon Ekpa.

Ya musanta zarge-zargen

Ekpa - da ke iƙirarin jagorantar gwamnatin Biafra daga inda yake gudun hijira - ya shiga hannu a watan Nuwamban bara.

Hukumar gabatar da ƙarar ta ce wanda ake zargin na ci gaba da zama a tsare kuma ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.

An san Ekpa da bayyana kansa a matsayin shugaban wani tsagi na Kungiyar ‘Yan Asalin Yankin Biafra, wanda ke neman kafa ƙasa a yankin kudu maso-gabashin Nijeriya, inda a ƙarshen shekarun 1960 aka gwabza yaƙin basasa da ya janyo asarar rayuka.

Ɗan ƙasar Finland kuma ɗan Nijeriya, ya kasance wakilin jam’iyyat NCP mai ra’ayin riƙau a garin Lahti, arewa da Helsinki a Finlad, inda ya yi aiki a matsayin mamba a kwamitin sufuri.

An janye zarge-zargen wasu

A lokacin da aka kama Ekpa, mahukuntan Finland sun buƙaci cewa akama wasu ƙarin mutane huɗu da ke zargi da ɗaukar nauyin ayyukan Ekpa.

A ranar Juma’a, hukumar gabatar da karar ta ce mai gabatar da ƙara ya yanke hukuncin janye tuhumar karin wasu mutane huɗu sabod ababu cikakkiyar shaida.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya sha bin diddigin abubuwan da Ekpa ke yi a ‘yan shekarun nan musamman kalaman karya da kage kan neman ‘yancin kai.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us