Hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya NDLEA ta yi nasarar kama ƙwayoyin tramadol miliyan biyu a Kano.
Hukumar ce ta sanar da haka a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce ta kai ga kama ƙwayoyin ne bayan jami’anta sun tare wata mota ƙirar Toyota Sienna kan hanyar Kano zuwa Jigawa.
Daga cikin abubuwan da aka kama a cikin motar akwai ƙwayoyi dubu ɗari biyu na ƙwayar tramadol da kafso 217,500 na pregabalin.
NDLEA ɗin ta ce bayan samun waɗannan ƙwayoyin ne suka bi diddiƙin ainahin dillalin ƙwayoyin a gidansa da ke Mil Tara a Kano inda suka gano ƙwayar tramadol 1,584,000 jibge a cikin wata mota ƙirar Nissan a gidansa.
Wannan ne ya kawo adadin ƙwayoyin da aka kama suka zama 2,001,500.
Ƙasa da mako guda bayan hukumar ta NDLEA ta gano ɗauri 20 na hodar ibilis a cikin littattafan addini da ake shirin kai su Saudiyya, hukumar ta sake kama wasu ɗauri 46 na hodar ibilis ɗin mai nauyin gram 547 a cikin man shafawa zuwa ƙasar da ke Gabas ta Tsakiya.
NDLEA ɗin ta ce ta kama hodar ne a ranar Laraba 23 ga Afrilu a wani kamfanin da ake jigilar kayayyaki a Legas. Ta ce baya ga hodar ibilis ɗin da aka gano a ranar, an samu kilo 1.8 na allurar pentazocine da kuma gram 60 na ƙwayoyin bromazepam waɗanda za a kai su Canada.
Ana yawan samun lamuran safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya amma hukumar ta NDLEA ta ce tana samun ci gaba matuka wurin daƙile waɗannan ayyuka.