Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano a Nijeriya ta sanar da dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango gar guda 22.
A sanarwar da ta fitar ranar Litinin 19 ga watan Mayun 2025, mai ɗauke da sa hannun Abdullahi Sani Sulaiman Jami'in yada labarai na hukumar, ta ce ta yi hakan ne a ƙoƙarinta na tabbatar dacewa ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara ɗora masana'antar Kannywood a kan saiti.
“Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba El-mustapha ta dauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ƙa'idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne fim gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al'umma inda ta dakatar da wasu manyan fina-finai har guda 22 daga saka su a kafafen Intanet ko gidajen talabijin,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa Abba El-mustapha ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami'an hukumar tare da dogon nazari domin kawo karshen ƙorafe-ƙorafen da hukumar take yawan karba don ƙara inganta ayyukan hukumar tare da masana'antar Kannywood.
Fina-finan da hukumar ta dakatar da nunawa sun haɗa da:
1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wa yasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Dadin Kowa
20. Tabarma
21. Kishiyata
22. Rigar Aro
Sanarwar ta ce doka ce ta bai wa hukumar damar tace duk wani fim tare da lura da ayyukan ‘yan masana'antar Kannywood matsawar suna da rajista da hukumar a ko ina suke.
“A saboda haka ana shawartar masu daukar nauyin waɗannan fina-finai da su tabbatar da sun bi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka waɗannan fina-finai a gidajen talabijin ko intanet.”
Haka kuma ana sanar da masu shirya fina-finan cewa su miƙa fina-finansu ga hukumar domin tantance su tare da ba su shaidar inganci ta tacewa nan da sati daya mai zuwa wato daga Litinin, 18 ga watan Mayu zuwa 25 ga Mayun 2025 domin gujewa fushin doka.
A karshe hukumar ta nemi hadin-kan dukkannin gidajen talabijin hukumar da ke lura da kafafen yada labarai ta Nijeriya wato NBC kan su cigaba da taimaka mata domin samun nasarar abin da ta saka a gaba da cigaban jihar Kano da masana'antar Kannywood.