Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana burin kasar Turkiyya na kara karfin wutar lantarkin da ta kafa na hasken rana da iska zuwa megawatt 120,000 nan da shekarar 2035, wanda ke zama wani babban mataki a yunkurin kasar na samun sauyi da ɗorewar makamashi.
Da yake jawabi a wajen bikin bude babban taron zuba jarin makamashi mai sabuntawa na shekarar 2024 a jiya Laraba, Erdogan ya ce fadada abubuwan da za a iya sabuntawa ya ta'allaka ne a kan dabarun makamashi na kasar Turkiyya, yana mai jaddada kudirin gwamnati na rage dogaro kan hanyoyin makamashin kasashen waje.
Ya tsara manufofin makamashi ba kawai a matsayin fifikon tattalin arziki ba har ma a matsayin batun tsaron kasa.
"Tsaron samar da kayayyaki, diflomasiyya ta makamashi, da bambance-bambancen albarkatu an fara daukar su ba kawai a matsayin batutuwan fasaha ba har ma da batutuwan da suka shafi tsaron kasa kai tsaye," in ji Erdogan.
Har ila yau, ya yi nuni da karuwar tashe-tashen hankula a duniya, yana mai cewa: "Ba za mu iya kallon tashin hankalin da ake samu a yankuna da dama na duniya, daga Afirka zuwa Asiya, da kuma daga Gabas ta Tsakiya zuwa Latin Amurka, a matsayin wani abu daban da buƙatar haɓaka samar da makamashi ba."
Da yake bayyana manufofin Turkiyya, Erdogan ya sake nanata burin kasar na rage shigo da makamashi daga ƙetare, rage kudin makamashinta, da kuma sanya kanta a matsayin mai fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a dukkan albarkatun kasa da fasaha.
Da yake karin haske kan abubuwan da suka faru a baya bayan nan, shugaban ya ce: "Mun sauya makomar al'ummarmu, tare da binciken da muka gano a cikin Tekun Habar Aswad da Gabar. Mun daukaka kasarmu zuwa wata kungiya ta daban, tare da aikin samar da makamashin nukiliya na Akkuyu."