28 Afrilu 2025
Sashen Sadarwa na Turkiyya ya musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai da ke cewa Ankara ta aike da jiragen sama shida ɗauke da makamai zuwa Pakistan.
A wata sanarwa a ranar Litinin ta shafin X, Cibiyar Yaƙi da yaɗa Labaran Ƙarya ta Sashen ta ce ikirarin, wanda ya ɓulla a wasu kafafen yaɗa labarai, ba gaskiya ba ne.
“Jirgin ɗaukar kaya daga Turkiyya ya sauka a Pakistan don ƙara mai. Bayan haka, jirgin ya tafi zuwa inda ya nufa.”
Sanarwar ta kara da cewa “Bai kamata a yi amfani da rahotannin jita-jita na waɗansu mutane ko hukumomi ba da ba su da hurumi.”