Firaministan Iraƙi Mohammed Shia al Sudani ya bayyana Aikin Hanyar Ci-gaba da Turkiyya-Iraki ke jagoranta matsayin “ɗaya daga ayyuka mafiya muhimmanci a Gabas ta Tsakiya,” yana mai cewa hakan zai sake fasalin haɗuwar yankin da haɓaka tattalin arziki.
Da yake jawabi a wajen taro mai taken “Hangen nesa: Alaƙar Turkiyya-Iraki” a babban birnin Ankara a ranar Alhamis, al Sudani ya ƙara da cewa gwamnatinsa na son alaƙar Turkiyya da Iraki su zama jigon zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
“Muna son alaƙar Turkiyya da Iraƙi su zama wani ɓangare na turakun zaman lafiya a yankinmu,” in ji shi, yana mai ƙarin haske kan muhimmancin haɗin kai tsakanin maƙotan biyu.
Sudani ya soki Firaministan Isra’ila tare da yin gargaɗin samun rikici a yankin. “Gwamnatin Netanyahu na ƙoƙarin jefa yankin a cikin yaƙi,” in ji shi.
A yayin taron da aka yi a hedkwatar Anatolia, Sudani ya yi bayani sosai game da alaƙar Turkiyya-Iraƙi, inda suke warware matsalolin da ke tsakaninsu, ba ma batutuwan yanki da ƙasa da ƙasa.
Manufar haɓaka kasuwanci zuwa na dala biliyan 30
Ministan Kasuwanci na Turkiyya Omer Bolat ya ce Turkiyya da Iraki za su ci-gaba da ɗaukar sabbin matakai na haɓaka kasuwancinsu zuwa dala biliyan 30, da ƙara yawan zuba jari a tsakaninsu.
“Na yi amanna cewa taron wakila da za a yi ƙarƙashin shugabancin shugabanmu Recep Tayyip Erdogan da Firaministan Iraƙi al Sudani zai bayar da ƙaƙƙarfar gudunmawa wajen haɓaka alaƙar Turkiyya-Iraƙi, suke ta sanun ci-gaba a ‘yan shekarun nan a fannonin siyasa, da tattalin arziki.
Ya kuma jaddada cewa za su ɗauki sabbin matakai don ƙarfafa alaƙa da kasuwancinsu da Iraki da Shirin Ci-gaba da sabbin kofofin kan iyaka.
“A wannan waje, ina maraba da Firaministan Iraki Mr al Sudan, zuwa ƙasarmu, muna kuma fatan wannan ziyara za ta bayar da gudunmawa ga alaƙar ƙasashenmu biyu,” ya ƙara faɗa.
Aikin Hanyar Ci-gaba babban aikin hanyar kasuwanci ne da ya haɗa Iraƙi da Turkiyya ta layin dogo, hanyoyin mota, tashoshin jiragen ruwa da garuruwa.
Aikin na da tsayin kilomita 1,200 (Mil 745), layin dogo da titunan mota za su hade da Tashar Jiragen Ruwa ta ‘Great Faw’, wadda za ta zama tashar jiragen ruwa mafi girma a gabas ta Tsakiya.