Oluwatobi Oyinlola: Ɗan Nijeriya ya kafa tarihin ƙirƙirar na'urar GPS mafi ƙanƙanta a duniya
Oluwatobi Oyinlola: Ɗan Nijeriya ya kafa tarihin ƙirƙirar na'urar GPS mafi ƙanƙanta a duniya
Na'urar GPS da Oluwatobi Oyinlola ya ƙirƙira tana da girma da faɗin milimita 22.93 x 11.92 ne kacal, kuma ta yi kusa da girman katin sim.
7 Mayu 2025

Wani matashi mai ƙirƙira daga Nijeriya ya kafa sabon tarihin a kundin bajinta na Guinness World Record, saboda ƙirƙirar wata ƙaramar na'urar GPS ta bin-sawu.

Na'urar GPS ɗin da Oluwatobi Oyinlola ya ƙera, tana da girma da faɗin milimita 22.93 x 11.92, kuma tana kusan daidai da girman katin SIM na wayar hannu.

Wannan ƙoƙari ya samu yabo a matsayin babban cigaba a fannin ƙera ƙananan kayan lantarki da na'urori.

“Oluwatobi ya yi amanna da ƙoƙarin ƙure iyaka wajen ƙirƙirar kayan fasaha, musamman wajen rage girman na’urori,” in ji Guinness World Records (GWR), a cikin wata sanarwa.

Fasahar Global Positioning System (GPS) tana bai wa masu amfani da ita damar bin-sawu da lura da wuraren da na'urorin da aka saka masu na’urorin karɓar sigina.

Wannan ƙirƙira ta samu ne daga binciken da Oluwatobi ke yi a Massachusetts Institute of Technology a Amurka. Kuma shi luwatobi an haife shi ne kuma ya tashi a garin Ibadan, da ke kudu maso yammacin Nijeriya.

Fasahar ceton-rai

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yaba da wannan ƙirƙira yana mai cewa tana da “hanyoyin amfani mara iyaka a fannoni daban-daban na rayuwa da masana'antu.’’

Shugaba Tinubu ya kuma nuna kyakkyawan fata kan damar matasan Nijeriya. “Muna taya murna ga Oluwatobi, kan wannan nasara. Ka nuna wa duniya cewa matasan Nijeriya za su iya!,” in ji shugaban a wani rubutu a dandalin X.

Ministan Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arziƙin Dijital na Nijeriya, Bosun Tijani, ya yaba wa matashin kan ƙirƙirar, yana mai cewa shi ne ke nun “babbar baiwa a cikin wannan fage”.

Ya kuma sake jaddada ƙudurin gwamnati na bunƙasa cigaban kimiyya da fasaha a ƙasar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us