‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane 50 a hare-hare daban-daban da aka kai a jihohi uku na arewacin Nijeriya, kamar yadda hukumomi da majiyoyin yankin suka tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Turkiyya na Anadolu a ranar Litinin.
Hare-haren sun faru ne a jihohin Katsina, Kebbi, da Benue a ranar Asabar da Lahadi, wanda ya sake nuna yadda matsalar tsaro ke kara ta'azzara a yankin.
Duk da cewa babu wata kungiya da ta dauki alhakin hare-haren, mutane da dama na zargin cewa ‘yan fashi ne suka kai su.
Wadannan ‘yan fashi sun shahara wajen aikata laifuka a arewacin Nijeriya tun daga shekarar 2020, inda suke amfani da tashin hankali, fashi, ko kuma garkuwa da mutane.
Sun zama babbar matsalar tsaro a Nijeriya, suna haifar da cikas ga al’ummomi da rayuwar jama’a.
A cewar mazauna yankin, an gano gawarwaki 20 a ranar Lahadi a al’ummar Gobirawa da ke karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina. An ce ‘yan fashi ne suka kashe su a daren Asabar.
An lalata shaguna da gidaje
Shaidun gani da ido da dama sun shaida wa Anadolu ta waya cewa maharan sun shiga al’ummar ne a kan babura suna harbin jama’a.
A cewar Abdurrahman Abdullahi, shugaban hadaddiyar kungiyar al’umma ta jihar Katsina kuma jagoran al’umma a Gobirawa, harin ya lalata shaguna 15 da gidaje 20.
“Bayan gawarwaki 20 da muka samu a ranar Lahadi, mutane da dama sun rasa matsugunansu wasu kuma sun ɓata,” in ji Abdullahi wa Anadolu.
Abubakar Sadiq Aliyu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da hare-haren ga Anadolu amma bai bayar da karin bayani ba. Rundunar ‘yan sandan jihar har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa kan hare-haren ba.
Manoma sun mutu a gonakinsu
A ranar Lahadi, an kashe manoma 15 a jihar Kebbi yayin da suke aiki a gonakinsu a kauyen Waje, karamar hukumar Danko Wasagu.
Aliyu Ahmad Wasagu, daya daga cikin manoman da ya tsira, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, lokacin da mazauna yankin suka yi tunanin an samu zaman lafiya a yankin.
“Harin ya faru ne lokacin da muka yi tunanin zaman lafiya ya dawo a al’ummomin Danko Wasagu,” in ji shi wa Anadolu.
Hussaini Aliyu Bena, shugaban karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa ‘yan ta’adda sun kashe mutane 15 kuma sun raunata wasu uku.
Kiraye-kiraye don magance rashin tsaro
A wani harin kuma, an kashe mutane 15 a ranar Lahadi da yamma a kusa da Ogwumogbo da Okpo’okpolo a karamar hukumar Agatu ta jihar Benue. Mafi yawansu ‘yan kasuwa ne.
A cewar Quadri Muniru, wani ɗan kasuwa da ya yi magana da Anadolu a daren Lahadi, wadanda abin ya shafa sun fada tarkon ‘yan fashi ne yayin da suke dawowa daga kasuwar Oweto.
Hare-haren sun sake jaddada bukatar daukar matakan tsaro masu karfi a al’ummomin da ke cikin hadari.
Gwamnatin Nijeriya na fuskantar ƙarin matsin lamba don magance matsalar rashin tsaro da ke kara ta’azzara a yankin, wanda ya haifar da mutuwar dubban mutane da kuma raba jama’a da muhallansu.