NIJERIYA
3 minti karatu
Gwamnan Borno ya roƙi gwamnatin Tarayyar Nijeriya kar ta bari Boko Haram ta ƙwace garin Marte
Zulum, wanda da shi aka yi ta tsare-tsaren ayyukan tsaro har cikin tsakar dare a ranar Asabar, ya gudanar da rangadi don tantance ƙalubalen da aka fuskanta a Marte, tare da lalubo hanyoyin da za a bi don samar da zaman lafiya.
Gwamnan Borno ya roƙi gwamnatin Tarayyar Nijeriya kar ta bari Boko Haram ta ƙwace garin Marte
Borno state Governor Babagana Umara Zulum addresses a past press briefing. Photo / X / Others
19 Mayu 2025

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta samar da ƙwararan dabarun da za su tabbatar da cewa garin Marte bai faɗa hannun mayaƙan Boko Haram da ISWAP ba.

Zulum, wanda da shi aka yi ta tsare-tsaren ayyukan tsaro har cikin tsakar dare a ranar Asabar, ya gudanar da rangadi don tantance ƙalubalen da aka fuskanta a Marte, tare da lalubo hanyoyin da za a bi don samar da zaman lafiya.

Kafin zuwan Zulum, duk jama’ar cikin garin Marte sun tsere gaba ɗaya bayan harin da mayaƙan Boko Haram suka kai ranar Juma'ar da ta gabata, inda dubbai suka fake a garin Dikwa.

Da yake magana da manema labarai a jiya Lahadi, gwamnan ya jaddada cewa ziyarar da ya kai Marte ta kasance domin samar da haɗin-kan al’umma, da juriya, da kuma ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro.

Ya ce, "A shekara huɗu da suka wuce ne aka sake mayar da al’ummar Marte garinsu, amma abin takaici, a cikin kwanaki ukun da suka gabata, an sake tarwatsa shi tare da saka mutanen garin yin gudun hijira."

“Mutane kusan 20,000 ne suka bar Marte zuwa Dikwa; wannan adadi mai yawa barazana ce domin barinsu su zauna a sansanin na iya sanya mafi akasarin matasa su shiga cikin mawuyacin hali da kuma yiwuwar masu tayar da ƙayar bayan sun sanya su a cikinsu,” in ji gwamnan.

“Alhamdulillah jiya mun dawo Marte muka kwana tare da goyon bayan sojojin Nijeriya da ‘yan sa-kai, yanzu haka an sake tsugunar da al’umma a karo na biyu, duk da haka roƙona ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da sojojin Nijeriya shi ne mu yi duk mai yiwuwa domin ganin ba a ƙwace wannan gari ba.

“Kawo yanzu Karamar Hukumar Marte ta ƙunshi garuruwa da ƙauyuka sama da 300, a yanzu muna da matsayi ɗaya kawai, idan ba za mu iya kula da wannan ba, to za mu rasa dukkanin ƙananan hukumomin ga ‘yan tayar da ƙayar baya, wanda hakan zai yi matukar tayar da hankali, kuma ina ganin ba za mu bari hakan ya faru ba, don haka ina kira ga Gwamnatin Tarayya da Rundunar Sojojin Nijeriya, mu hada kanmu domin wannan gari ya ci gaba da zama a hannunmu.”

Gwamnan ya jaddada ƙudirinsa na tallafa wa jami’an tsaro wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar Borno, inda ya ce, “A bangarena a matsayina na gwamnan jihar Borno, zan yi duk mai yiwuwa wajen tallafa wa jiga-jigan sojojinmu a kokarinsu na samar da dauwamammen zaman lafiya a jiharmu da muke so.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us