NIJERIYA
2 minti karatu
Boko Haram: Majalisar dattawan Nijeriya ta nemi a tura ƙarin sojoji Borno da Yobe
Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin Nijeriya, ciki har da kisan sojoji a garin Marte.
Boko Haram: Majalisar dattawan Nijeriya ta nemi a tura ƙarin sojoji Borno da Yobe
Kazalika majalisar ta nemi kwamitinta kan sojin ƙasa da na sama ya sa ido tare da tabbatar da cewa sojojin sun bi umarnin. / TRT Afrika Hausa
14 Mayu 2025

Majalisar dattawan Nijeriya ranar Talata ta buƙaci rundunar sojin ƙasar ta ƙara tura sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin. 

Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da ke ƙaramar hukumar Monguno a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, da kuma wani harin da suka kai Gajiram, fadar ƙaramar hukumar Nganzai, a safiyar ranar Talata.

A ƙudurin da mai tsawatarwa a majalisar, Sanata Tahir Munguno, ya gabatar, ya ce ‘yan majalisar sun yi nuni da yadda a baya kashi biyu cikin uku na ƙananan hukumomin jihar Borno suka kasance ƙarƙashin ikon ‘yan Boko Haram, inda haɗin kai tsakanin sojoji da ‘yan sa kai ya taimaka wajen ƙwato ƙananan hukumomin.

Amman zaman lafiyan da aka samu, ya sa hedikwatar yaƙi da ta’addancin ta koma arewa maso yammacin ƙasar inda sojin ƙasar ke yaƙi da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Yayin da yake nuna damuwa game da yadda ‘yan ta’addan ke sauya dabarun yaƙinsu, Monguno ya bayyana yadda ƙungiyar ke amfani da na’urorin zamani ciki har da jirage mara matuƙa da kuma ƙarin amfani da abubuwan fashewa da suka ƙera da kansu, lamarin da ya janyo mace-macen fararen hula da sojoji da kuma katse harkokin sufuri.

Bayan haka ne majalisar dattawan Nijeriyar ta yi kira ga shugabannin sojin ƙasar su tura isassun sojoji zuwa arewa maso gabashin ƙasar su kuma tabbatar da cewa an ba su na’urorin zamani domin su daƙile sabuwar barazanar.

Kazalika majalisar ta nemi kwamitinta kan sojin ƙasa da na sama ya sa ido tare da tabbatar da cewa sojojin sun bi umarnin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us