Me ya sa masu fasa-kwauri suka koma safarar tururuwa, baya ga hauren giwa?
Me ya sa masu fasa-kwauri suka koma safarar tururuwa, baya ga hauren giwa?
Wasu mutane sukan samu annashuwa daga kallon dandazon tururuwa yayin da suke gina gidanjensu, abin da ya haifar da samuwar kasuwancin ƙananan ƙwarin ɗebe kewa, wanda ke juya akalar masu fasa-ƙwaurin hauren giwa zuwa ƙananan halittu.
13 Mayu 2025

Ga mutane da dama, tururuwa wata ƙaramar halitta ce mara muhimmanci. Amma akwai nau’in tururuwar Afirka mai jidon iri, wadda ake kira “African harvester ants” waɗanda ba za a saka su cikin marasa muhimmanci ba.

Bayan da ‘yan-sandan Kenya suka bankaɗo wani gungun masu fasa-ƙwauri, yanzu ta bayyana cewa akwai wata kasuwar dabbobin ɗebe kewa ta bayan-fage, wadda ke da girman darajar, wato safarar tururuwa don masu neman ƙure nishaɗinsu.

An samu wasu mutane biyu ‘yan Belgium, da wani ɗan Vietnam, da ɗan Kenya, bisa laifin fasa-ƙwaurin riƙaƙƙun sarauniyar tururuwa kimanin 5,440, waɗanda masu gabatar da ƙara a Kenya suka ƙiyasta darajarsu ta kai kusan shilling miliyan 1.2 na Kenya ($9,300).

Hasali ma, farashin tururuwar a kasuwannin Birtaniya yakan kai har dala miliyan $1, matuƙar suka isa iyakokin Turai. Kuma an ƙiyasta kowace tururuwa sarauniya da aka ƙwace ta kai darajar kusan dala $233.

Dino Martins, Daraktan Turkana Basin Institute, kuma ɗaya daga cikin manyan masana ƙwari a Kenya ya ce, "Hajar tururuwa ta zama tamkar hodar ibilis. Akwai kamanceceniya tsakanin farashin koken a Colombia, idan aka kwatanta da kilogram na tururuwar a kasuwanin Turai, shi ya sa mutane ke yin safarar."

Dabbobin ado na ƙure nishaɗi

Masoya tururuwa sukan kashe kuɗi masu yawa don kula da gidan tururuwa da ake yi cikin kwantena da ake iya ganin abin da ke ciki, don su iya ganin ayyuka da al’adun tururuwa.

"Waɗannan ƙwari sukan gina gidaje gwanin ban sha’awa sosai," in ji Edith Kabesiime, Manajan Kamfen na Kare Dabbobin Daji, a zantawarsa da TRT Afrika.

"Wasu mutane suna kallon rayuwar tururuwa don samun nishaɗantarwa. Suna samun farin ciki daga kallon su."

Wannan tsantsar farin ciki da suke samu yanzu yana haifar da wata harka ta masu kasuwancin irin waɗannan ƙananan halittu masu daraja, wadda kimar kasuwancin ta kai biliyoyin daloli.

Ba a bayyana ba ko wannan yunƙurin fasa-ƙwauri ta filin jirgin saman Jomo Kenyatta na Nairobi wani yunƙuri ne na masu sha'awa marasa ƙwarewa, ko kuma wata babbar ƙungiyar masu fasa-ƙwauri ce da ke binciken sabbin hajojin kasuwanci da sabbin kasuwanni.

Duk da haka, masu kare muhalli suna ganin wannan kamar wani babban sauyi ne a tsarin fasa-ƙwauri daga fannin manyan dabbobin daji, zuwa ƙananan halittu masu matuƙar muhimmanci ga muhalli.

"Muna ganin ƙungiyoyin masu laifi suna faɗaɗa safararsu daga farautar hauren giwa zuwa dukkanin nau'ikan halittu - daga tsirrai don yin magani, zuwa ƙwari, zuwa ƙananan halittu," in ji Erustus Kanga, daraktan janar na KWS a cikin wata sanarwa.

"Mu ba masu laifi ba ne, mu ‘yan shekaru 18 ne masu aiki rashin sani. Kuma burinmu kawai mu koma gida don sake fara rayuwa," in ji ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, David Lornoy, ɗan Belgium, a lokacin shari'ar.

Amma Samuel Mutua, masanin laifukan dabbobin daji na International Fund for Animal Welfare, ya ce wannan lamari na safarar ƙwari ya cancanci a kira shi shiryayyen laifi. "Ko da kuwa shekarunsu ƙanana ne, sun sami nasarar tattara ƙwari masu yawa," in ji shi.

Muhimmanci ga muhalli

Idan da waɗannan ƙwari kamar tururuwa za su ɓace daga doron duniya ko kuma adadinsu ya ragu sosai, to abubuwa da dama za su sauya a muhallin duniyarmu.

"Kamar yadda sunansu ya nuna, “harvester ants” masu jidon iri ne, kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen rarraba iri da tsirrai a muhalli," in ji Kabesiime.

"Idan ka taɓa ganin su, za ka lura suna ɗaukar iri zuwa gidajensu da wasu wurare, wanda ke taimakawa wajen yaɗuwar ƙwayar iri."

A cewar Martins daga Turkana Basin Institute, tururuwar harvester ants, waɗanda aikinsu ya kasance cikin labarin hikimar Annabi Sulaimana a Littafi Mai Tsarki, suna kiyaye lafiyar ƙwarin yankin Rift Valley na Kenya, ta hanyar rarrabawa da haɗa iri na ciyawa a faɗin filin muhalli ko dazuka.

"Idan da za mu rasa dukkan giwaye a Afirka, za mu shiga damuwa, amma filin ciyawar daji zai ci gaba da wanzuwa. Amma idan da za mu rasa dukkan ƙwarin tururuwar jido, da kwarkwasa, to kuwa ciyayi za su daina fitowa a yankin savannah," in ji Martins.

Tururuwar jido na zaune a cikin ƙasa, suna ta haƙa ramuka da gina gidajensu, a wani tsari da ke sanya iska a cikin ƙasa, da haɗa sinadaran abinci a ciki, wanda hakan ke taimakawa tsirrai su girma.

Kabesiime ya ƙara da cewa, "Idan da ba tare da su ba, za a samu raguwar bambancin halittu, kuma zai shafi girman tsirrai saboda raguwar iska a cikin ƙasa".

Tururuwa jinsin “Giant African harvesters” suna aiki a matsayin masu tsaftace muhalli, suna taimakawa wajen ruɓewar abubuwa da samar da ƙasar da tsirrai ke dogara kanta.

Sarauniyar ƙwari

Bayan gudunmawarsu mai muhimmanci wajen ginuwar albarkar ƙasa, tururuwar na taimakawa wajen kula da tarwatsa wasu ƙwari masu cutarwa.

"Wani lokaci za ka ga suna kawar da wasu ƙwari, wanda hakan ke taimakawa wajen maganin ƙwari masu cutarwa a wuraren noma. Haka nan kuma suna zama abinci ga wasu nau'ikan halittu kamar tsuntsaye, dabbobin ruwa, da sauran halittu masu dogaro da ƙananan ƙwari."

Wannan ya sa masu kare muhalli, suke ganin, ƙahon zuƙar da aka saka wa nau’in “tururuwa sarauniya” babban abin damuwa.

Sarauniyar tururuwa na da matuƙar muhimmanci ga kowane gidan tururuwa, saboda su ne kaɗai ke iya yin ƙwai wanda ke haifar sojojin tururuwa, da sojoji, da sabuwar sarauniya ta gaba.

Wannan ne dalilin da ya sa fasa-ƙwauri sarauniyar tururuwa ke iya jefa gidajen turuwa cikin haɗari.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us