NIJERIYA
2 minti karatu
Mele Kyari: EFCC ta yi wa tsohon shugaban NNPCL tambayoyi
EFCC tana bincike ne kan yadda aka kashe kimanin dala biliyan biyu a gyaran matatun mai na Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari.
Mele Kyari: EFCC ta yi wa tsohon shugaban NNPCL tambayoyi
Kyari ya ce dole EFCC su yi nasu aikin domin Nijeriya ta ci gaba / NNPCL
11 Satumba 2025

Tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ranar Laraba ya je hedkwatar hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar ta’annati (EFCC) domin amsa tambayoyi kan yadda ya tafiyar da harkokin kuɗi a lokacin da yake shugabanci a kamfanin.

Bayanai sun nuna cewa Kyari ya isa hedkwatar EFCC a Abuja da misalin ƙarfe 2:15 na ranar Laraba.

Rahotanni daga kafofin watsa labaran Nijeriya sun ce EFCC tana bincike ne kan yadda aka kashe kimanin dala biliyan biyu a gyaran matatun mai na ƙasar a ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari, waɗanda suka haɗa da dala biliyan 1.55 da aka kashe a kan Matatar Mai ta Fatakwal, da dala miliyan 740.6 a Matatar Kaduna da kuma dala miliyan 656.9 a Matatar Warri.

Yayin da ya isa hedkwatar EFCC, an ambato tsohon shugaban na NNPCL  yana cewa, “Na yi nawa [aikin]; dole EFCC su yi nasu. Idan ko wannenmu ya yi nasa aikin—ba tare da tsoro ko alfarma ba, cikin gaskiya, da girmamawa da jajircewa—Nijeriya za ta ci gaba.”

Sai dai daga bisani bayanai sun tabbatar da cewa Mele Kyari ya bar hedkwatar hukumar ta EFCC.

A watan jiya ne wata babbar kotun Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ke Abuja ta ba da umarnin hana amfani na wucin-gadi da asusun banki huɗu da ke da alaƙa da tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya, NNPCL, Mele Kyari bisa zarge-zargen almundahana.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya ba da umarnin ne bayan lauyar hukumar EFCC, Ogechi Ujam, ta nemi kotun ta hana amfani da asusun guda huɗu na bankin Jaiz zuwa lokacin da hukumar za ta kammala bincike.

Alƙalin, a hukuncin da ya yanke, ya ce EFCC tana da hujja mai ƙwari, saboda haka ya amince da buƙatarta.

A watan Afrilun da ya gabata ne shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sauke Mele Kyari daga shugabancin NNPCL a wani mataki na yin gagarumin garambawul ga kamfanin.

An maye gurbinsa da Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin man.

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne ya naɗa Mele Kyari a matsayin shugaban kamfanin mai na ƙasar NNPC a shekarar 2019 bayan Maikanti Baru ya yi ritaya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us