WASANNI
2 minti karatu
Alonso zai gaji Ancelotti bayan ajiye aiki a Bayer Leverkusen
Kocin Bayer Leverkusen, Xabi Alonso na dab da ajiye aiki a ƙungiyar, domin komawa horar da Real Madrid.
Alonso zai gaji Ancelotti bayan ajiye aiki a Bayer Leverkusen
/ AFP
28 Afrilu 2025

Rahotanni daga Jamus na cewa kocin Bayer Leverkusen, Xabi Alonso na dab da ajiye aiki a ƙungiyar, domin komawa Real Madrid ta Sifaniya don maye gurbin Carlo Ancelotti.

A ƙarshen kakar bana ne Alonso zai yi ƙaura, kasancewar yana da damar amfani da wata saɗara a kwantiraginsa da leverkusen inda zai koma Madrid a matsayin koci mara ƙungiya.

Ita kuwa Real Madrid tana fuskantar kakar wasa ba tare da ɗaga kofi ba a bana, bayan an fitar da ita daga gasannin Zakarun Turai da na Copa Del Rey.

A yanzu La Liga ce ta rage mata, amma sai idan ta iya cim ma Barcelona, wanda abu ne mai matuƙar wahala ganin cewa wasanni biyar ne suka rage kafin kammala gasar.

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti yana shan suka kan raunin da ƙungiyar ta samu, kuma ana kyautata zaton zai bar ƙungiyar, inda kocin Leverkusen ke kan gaba a jerin masu neman kujerarsa.

Ancelotti zai koma horar da tawagar ƙwallo ta ƙasar Brazil, bayan da rahotanni suka bayyana cewa ya samu tayi daga hukumomin ƙwallo na ƙasar.

Mafita daga Jamus

Sai dai duk da cewa a bayyane take Xabi Alonso ɗan asalin Sifaniya ne zai karɓi ragamar Real Madrid, Alonso yana da ragowar kwantiragi a Bayer Leverkusen har zuwa kakar 2026.

Shafin Goal ya ambato shafin Sky France yana cewa Alonso yana da wata mafita a kwantiraginsa, inda akwai wata saɗarar da za ta ba shi damar ficewa daga ƙungiyar idan Madrid ta neme shi.

A halin yanzu, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Xabi Alonso da Real Madrid, sai dai akwai tarin sharuɗɗa da suka rage a samu matsaya kansu. Amma ana sa ran za su daidaita kan kwantiragin shekara biyu.

Idan Alonso ya karɓi Real Madrid a bazarar nan, akwai aiki a gabansa saboda tawagar tana fama da rashin daidaito, sannan ga batun ƙarancin haɗin-kai tsakanin ‘yan wasa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us