GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Isra'ila ta kashe iyalan mutum guda a Gaza
Iyalan mutumin sun rasu a lokacin da sojojin Isra'ila suka jefa bam ta sama a gidansu da ke kusa da tashar al-Attar a Khan Younis.
Isra'ila ta kashe iyalan mutum guda a Gaza
Tun daga Oktobar 2023, kisan kiyashin da Isra’ila ke aikatawa a Gaza ya yi sanadin mutuwar mutum 52,495 da kuma jikkata  118,366. / Reuters
4 Mayu 2025

Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai Khan Younis da ke Gaza a ranar Lahadi da safe ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla shida da jikkata wasu da dama.

Daga cikin waɗanda suka rasu har da iyalin mutum guda baki ɗayansu waɗanda suka haɗa da matar Munnir Qannan da ‘ya’yanta baki ɗaya.

Sun rasu ne a lokacin da Isra’ila ta jefa bam a gidansu da ke kusa da tashar al-Attar.

Haka kuma akwai wani bafalasɗine da ya rasu a cikin iyalan Basem al-Najjar a lokacin da bam ɗin Isra’ila ya faɗa kan tantinsu.

Haka wata mata ita ma ta rasu a harin da Isra’ilar ta kai a unguwar al-Amal.

Sai kuma wasu mutum shida da suka jikkata, inda biyu daga ciki suke cikin rai-kwakwai mutu-kwakwai a al-Qarara.

Tun daga Oktobar 2023, kisan kiyashin da Isra’ila ke aikatawa a Gaza ya yi sanadin mutuwar mutum 52,495 da kuma jikkata  118,366.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us