Attajiran Nijeriya Aliko Dangote da Femi Otedola da Mike Adenuga da Abdulsamad Rabiu suna cikin jerin attajiran duniya da suka mallaki sama da dala biliyan ɗaya a shekarar 2025, kamar yadda Mujallar Forbes ta wallafa.
Mujallar Forbes ta wallafa jerin sunayen ne ranar Asabar. Attajiran Nijeriya huɗu su kaɗai ne ‘yan ƙasar da sunayensu ke cikin jerin mutanen.
Alhaji Aaliko Dangote, wanda shi ne mai matatar Dangote yana saman jerin sunayen attajiran Afirka inda arzikinsa ya kai ga dala biliyan 23.9 a shekarar 2025, daga dala biliyan 13.9 da yake da shi a shekarar 2024.
“Aliko Dangote na Nijeriya shi ne a saman jerin sunayen a karo na 14 a jere inda arzikinsa ya kai dala biliyan 23.9, daga dala biliyan 13.9 shekara ɗaya da ta wuce,” in ji Mujallar. “Ƙara kimar matatar mansa da ta fara aiki kusa da Legas bayan jinkiri mai yawa a bara da Forbes ta yi cikin lissafin arzikinsa shi ne silar ƙarin da aka samu a yawan arzikinsa.”
Kazalika Mujallar Forbes ta ce Adenuga, shugaban kamfanin sadarwa na Globacom, ya zo na biyar, inda arzikinsa ya kai dala biliyan 6.8.
Abdulasamad Rabiu shugaban kamfanin BUA ya samu mataki na shida a nahiyar Afirka inda aka yi ƙiyasin cewa arzikinsa ya kai dala biliyan 5.1.
Shugaban bankin First Bank of Nigeria (FBN), shi ne ya zo na 16 a nahiyar inda arzikinsa ya kai dala biliyan 1.5.
“Wani biloniya wanda arzikinsa ya ƙaru da kashi 30 cikin 100: Femi Otedola na Nijeriya (mataki na 18, mai dala biliyan 1.5 ), shi ne shugaban kamfanin samar da makamashi na Geregu Power Plc wanda aka fara sayar da hannayen-jarin kamfanin,” kamar yadda Mujallar Forbes ta bayyana Otedola.
“Darajar hannayen-jarin kamfanin ta yi tashin da ya kai kashi 40 cikin 100 cikin shekarar da ta gabata bayan ƙarin da kamfanin ya samu na kuɗin shiga da riba. Attjiran Afirka biyu da a baya suka faɗo daga cikin jerin sunayen attajirai, yanzu sun sake komawa cikin jerin sunayen.”
Mujallar Forbes ta ce ƙasar Afirka ta kudu ta fi ko wace ƙasa yawan attajirai masu biliyoyin kuɗi cikin jerin sunayen attajiran inda take da attajirai bakwai.
Nijeriya da Masar na bin bayan Afirka ta kudu inda ko wannensu ke da attajirai huɗu-huɗu.
“Jerin sunayen attajiran ya kuma ƙunshi attajirai uku daga Maroko da kuma ɗaya daga Aljeriya (Isaad Rebrab ), inda Tanzaniya (Mohammed Dewiji) da Zimbabwe (Masiyiwa) ke da ɗaɗɗaya,” in ji mujallar tana mai ƙarawa da cewa “shekarar mai nasara ce ga attaijiran Afirka inda jumullar arzikinsu ya zarce dala biliyan 100 a karon farko a tarihi”.
“Attajiran Afirka 22 sun yi nasarar ƙara arzikinsu zuwa dala biliyan 105, daga dala biliyan 82.4 da kuma attajirai 20 na bara. Ba ƙaramar nasara ba ce a samu irin wannna mataki na ƙarin arziki a nahiyar, inda ake fama da rashin tabbas na siyasa da taɓarɓarewar darajar kuɗaɗe da kuma matsalar ciniki a kasuwar ababen amfanin yau da kullum,” in ji mujallar.