NIJERIYA
2 minti karatu
'Yan Boko Haram sun kashe fararen-hula 10 da 'yan bijilanti biyu a Borno
Mayaƙan na Boko Haram sun kashe mutanen ne a ƙauyen Bokko Ghide da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza, kamar yadda Sarkin na Gwoza ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
'Yan Boko Haram sun kashe fararen-hula 10 da 'yan bijilanti biyu a Borno
A kwanakin baya ne gwamnan Borni Babagana Zulum ya koka kan farfaɗowar hare-haren Boko Haram / TRT Afrika Hausa
27 Afrilu 2025

Mayaƙan Boko Haram sun kashe aƙalla mutum 12 a ƙauyen Bokko Ghide da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.

Sarkin Gwoza Mohammed Timta ne ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Lahadi da safe.

Ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun yi kwanton-ɓauna ga ‘yan bijilanti biyu a kan hanyar Kirawa da ke gundumar Pulka, inda sauran mutum goman kuwa fararen hula ne waɗanda suka shiga daji domin neman itacen da za su yi girki.

 “Duk da cewa mun binne waɗanda suka rasu, amma har yanzu akwai sauran waɗanda suka jikkata da suke samun kulawar asibiti a Maiduguri,” kamar yadda Timta ya bayyana.

“Mutane a halin yanzu na tsoron zuwa gonakinsu, kuma yanzu lokaci ne na shirya wa aikin gona kafin samun isashen ruwan sama,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Hare-haren dai na zuwa ne a ƙasa da kwana biyu bayan Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aika da ministan tsaro Badaru Abubakar, da Babban Hafsan Soji Janar Christopher Musa, da wasu manyan kwamandojin soji domin su duba halin tsaro a jihar Borno bayan da gwamna Babagana Zulum ya yi gargaɗin cewa hare-haren ‘yan ta’adda na sake farfaɗowa haka kuma lamarin na ƙara ƙamari a yankin Tafkin Chadi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us