Saudiyya da Qatar sun bayyana cewa za su biya bashin da Bankin Duniya ke bin Siriya wanda ya kai dala miliyan 15.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar ranar Lahadi, ƙasashen biyu sun ce biyan bashin da Bankin Duniya ke bin Siriya zai taimaka wajen murmurewar ƙasar cikin sauri.
"Hakan kuma zai ba da damar samun tallafin kuɗi nan gaba don ci-gaban muhimman ɓangarori, tare da tallafin fasaha da zai taimaka wajen sake gina cibiyoyi da bunƙasa ƙwarewa, da tsara manufofi da gyare-gyare don inganta ci-gaba," in ji sanarwar.
Ƙasashen biyu sun yi kira ga cibiyoyin kuɗi na ƙasa da ƙasa da na yankin da su "gaggauta ci gaba da faɗaɗa ayyukan bunƙasa Siriya, su haɗa ƙarfi da ƙarfe, kuma su tallafa wa duk wani abu da zai taimaka wajen cim ma burin 'yan uwantaka na al'ummar Siriya don makoma mai kyau."
Gwamnatin wucin-gadi
Gwamnan babban bankin Siriya da ministan kuɗin ƙasar sun halarci taron bazara na IMF da Bankin Duniya a makon da ya gabata, wanda shi ne karo na farko cikin fiye da shekaru 20.
A ranar Alhamis, Daraktar IMF Kristalina Georgieva ta bayyana cewa IMF na da niyyar taimaka wa Siriya wajen sake gina cibiyoyinta da kuma dawo da ita cikin tattalin arzikin duniya.
Bashar Assad, wanda ya mulki Siriya tsawon kusan shekaru 25, ya gudu zuwa Rasha a watan Disamba, wanda ya kawo ƙarshen mulkin jam'iyyar Baath da aka fara tun shekarar 1963.
An kafa gwamnatin wucin-gadi a ƙarshen watan Janairu, inda aka rushe kundin tsarin mulki, da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai, da majalisar dokoki, da jam'iyyar Baath.