logo
hausa
Labaranmu Na Yau, 15 ga watan Mayun 2025
03:58
Labaranmu Na Yau, 15 ga watan Mayun 2025
Nijeriya na bukatar $10B a duk shekara har tsawon shekaru 20 don samun wadatacciyar wutar lantarki sannan za a ji cewa Amurka ta taso keyar 'yan Nijeriya 6 zuwa gida bisa laifuka daban-daban

Kotu ta tsawaita wa'adin zaman gidan kaso wa tsohon shugaban Mauritania

Kotun ɗaukaka ƙara a Murtania ta zartaswa tsohon shugaban ƙasar Mohamed Ould Abdel Aziz ɗaurin shekaru 15 a gidan kaso, bayan da ya ɗaukaka ƙara akan hukuncin ɗaurin shekaru biyar da aka yanke masa, bisa aikata laifin karkata wasu kuɗaɗe shekaru biyu da suka gabata.

Tsohon shugaban, wanda ke ɗaure a gidan kaso tun hukuncin farko da aka yanke masa a watan Janairun 2023, ya bayyana a gaban kotu ne tare da ƙusoshin gwamnatinsa da suma ke fuskantar tuhume-tuhume akan amfani da matsayi wajen wadaƙa da dukiyoyin al’umma.

Akwai Ƙari Don Sauraro
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us