Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya Babagana Umara Zulum, ya bayyana shirin sake tsugunar da iyalai 6,000 daga sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke Maiduguri, saboda karuwar miyagun ayyuka da suka hada da karuwanci da cin zarafin yara da dai sauransu.
A ziyarar da ya kai sansanin, wanda ke dauke da iyalai kusan 11,000 da suka rasa matsugunansu, Zulum ya jaddada cewa sake musu matsugunan na da matukar muhimmanci wajen dakile munanan dabi'u da kuma samun zaman lafiya mai dorewa.
Ya ma nanata cewa mayar da jama’a zuwa yankunansu shi ne mabudin murkushe mayakan kungiyar Boko Haram.