Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya miƙa ƙorafe-ƙorafe guda uku na neman cire Alƙaliyar Alƙalan ƙasar Gertrude Araba Esaaba Sackey Torkornoo ga Majalisar Magabata domin ta yi nazari, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya zayyana.
Wata sanarwa da Mr Felix Kwakye Ofosu, mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar ta ce mutane daban-daban ne suka miƙa ƙorafe-ƙorafe na neman cire Alƙaliyar Alƙalan.
Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwaito cewa matakin wani ɓangare na soma bin tsarin cire Alƙaliyar Alkalan kamar yadda Layi na 146 na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasar na 1992 ya tsara.
Ana sa rai Majalisar Magabata ta Ƙasa za ta bai wa shugaban ƙasar shawara kan matakai na gaba da zai bi wajen cire ta kamar yadda doka ta tanada.
Sanarwar ba ta fayyace takamaimai ƙorafe-ƙorafen da ake yi a kanta ba.
An rantsar da Mai Shari’a Torkornoo a matsayin Alƙaliyar Aalƙalan Ghana ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2023, inda ta maye gurbin Mai Shari’a Kwasi Anin Yeboah, wanda ya yi ritaya a watan Mayu na 2023.
Kafin a naɗa ta kan muƙamin, Mai Shari’a Torkornoo ta yi aiki a matsayin Alƙaliyar Kotun Ƙoli, bayan ta shiga cikin jerin alƙalan kotun a shekarar 2019.