Wani taron siyasa a ƙasar Mali ya ba da shawarar bai wa shugaban mulkin sojan ƙasar, Assimi Goita muƙamin Shugaban ƙasa na shekara biyar.
Goita ya ƙwace mulki bayan jerin juyin mulkin da aka yi a shekarar 2020 da 2021.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa taron ya amince da hakan ne a wata sanarwar da ya fitar ranar Talata.
Bayan tattaunawar da aka yi a babban birnin ƙasar Bamako, taron ya kuma ba da shawarar rusa dukkan jam’iyyun siyasa, tare da tsaurara sharruɗan kafa sabbin jam’iyyu.
Ana sa ran za a aiwatar da shawarwarin da taron ya bayar cikin kwanaki masu zuwa.
Ɗaga girma
Goita, mai shekara 41, wanda ya kasance kanar a lokutan da aka yi juyin mulkin da ya kai shi ƙaragar mulki, ya samu ƙarin girma zuwa matakin Janar mai anini biyar a watan Oktoban shekarar 2024.
Ya kasance shugaban riƙon-ƙwarya na Mali tun shekarar 2021.
Daga farko dai shugabannin sojin ƙasar da ke yankin Sahel sun yi alƙawarin gudanar da zaɓe a watan Fabrairun shekarar 2022, wa’adin da aka ɗaga sama da sau ɗaya.
Sun sha alwashin yaƙar rashin tsaro a ƙasar ta Yammacin Afirka, inda ƙungiyoyi masu iƙirarin jahadi da ke da alaƙa da IS da Al-Qaeda suka shafe sama da shekara 10 suna aika-aika bayan sun fito daga cikin ‘yan tawayen Tuareg a arewacin ƙasar.