Gidan talbijin na Sudan ranar Alhamis ya ce sojojin ƙasar na dab da karɓe iko da Fadar shugaban ƙasar a Khartoum daga hannun dakarun rundunar RSF, lamarin da ya kawo wani babban sauyi a yaƙin da aka yi shekara biyu ana gwabzawa wanda yake barazanar raba ƙasar.
A yammacin ranar Laraba, an yi musayar wuta a kusa da fadar shugaban ƙasar, inda aka ji fashewar abubuwa da kuma hare-haren sama da sojin ta kai tsakiyar Khartoum, kamar yadda shaidu da kamfanin dillancin labaran Reuters suka ruwaito.
Ɓangarorin biyu na soji sun yi juyin mulki a shekarar 2021, lamarin da ya katse shirin miƙa mulki ga farar-hula, kuma yaƙi ya ɓarke a watan Afrilun shekarar 2023 bayan wani sabon shirin miƙa mulki ga farar-hula ya janyo rikici.
Yaƙin ya janyo abin da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ke kira matsalar jinƙai mafi girma a duniya da kuma ƙeta haƙƙin ɗan’adam mai yawa.