An rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Gabon Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban mulkin farar-hula na Gabon.
Mista Oligui wanda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo ƙarshen mulkin iyalan Bongo na gomman shekaru, ya sha rantsuwar kama aiki bayan ya jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya ta watanni 19.
Shugabannin ƙasashen Afirka da dama ne suka halarci bikin rantsuwar wanda aka yi a filin wasa mai ɗaukar mutum 40,000 da ke arewacin babban birnin kasar Libreville.
Daga cikin shugabannin da suka halarci taron akwai Adama Barrow na Gambia, Bassirou Diomaye Faye na Senegal, Ismail Omar Guelleh na Djibouti da Teodoro Obiang Nguema Mbasogo daga Equatorial Guinea.
Haka shi ma Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya samu wakilcin mataimakinsa Kashim Shettima a wurin bikin rantsuwar.
Shi ma shugaban Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo Felix Tshisekedi ya halarci taron tare da takwaransa na Rwanda Paul Kagame.
An ba da tikitin halartar taron a kyauta wanda aka yi a filin wasa na Angondje, wanda aka gina don girmama abokantaka tsakanin Gabon da China, kuma wannan shi ne karon farko da kasar ta gudanar da bikin ranstuwa a gabon ɗimbin jama’a haka
Baya ga rantsuwa, an shirya gudanar da wasu abubuwa na nishaɗi waɗanda suka haɗa da faretin soji.