Fararen fata 'yan Afirka ta Kudu da suka amince su koma Amurka da zama ba su fuskanci "kowane nau'in cin zarafi" a Afirka ta Kudu ba, in ji ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu a wata sanarwar da fitar ranar Litinin.
Wannan na zuwa ne bayan wasu ‘yan sa'o'i da rukunin farko na fararen fata 'yan Afirka ta Kudu 49 suka tashi daga birnin Johannesburg sakamakon tayin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na bai wa farare 'yan Afrikan damar zama a kasar a matsayin 'yan gudun hijira.
Mafi yawa daga cikinsu dai jikoki ‘yan Holland ne mazaunan, Trump ya ce ‘yan Afrika farar fata na fuskantar "wariyar launin fata" a Afirka ta Kudu, lamarin da ke ƙara rura wutar saɓanin tsakanin kasashen biyu.
"Ba za su iya ba da wata shaida ta kowane irin cin zarafi ba saboda babu wani nau'i na zalunci ga farar fata a Afirka ta Kudu ko 'yan Afirka ta Kudu farar fata," kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Ronald Lamola ya shaida wa manema labarai.
Iƙirarin da suka yi na cewa ana kai wa manoma fararen fata hari wani lokacin ma har da kisan kai, duk da bayanan da hukuma ta bayar na cewa galibin waɗanda ake kashewa matasa ne bakar fata a cikin birane- babu ƙanshin gaskiya a ciki, in ji ma’aikatar.
Zaluncin wariyar launin fata
Shugaban na Amurka, wanda aka haifi amininsa hamshakin attajirin nan Elon Musk a Afirka ta Kudu, ya bayyana a cikin watan Fabrairu cewa zai ba da fifikon samun damar shiga shirin 'yan gudun hijira "ga ‘yan Afrika farar fata na Afrika ta Kudu waɗanda ke fama da rashin adalci da wariyar launin fata".
"Mun yi farin ciki da cewa kungiyoyi da dama, hatta na Afrikaner, sun yi tir da wannan abin da aka kira zalunci ko cin zarafi," in ji Lamola.
Mutanen 49 ne suka bar babban filin tashi da saukar jiragen sama na Johannesburg a cikin wani jirgin haya a ranar Lahadi inda suka sauka a Amurka ranar Litinin.
Fararen fata ‘yan Afirka ta Kudu, waɗanda yawansu ya kai kashi 7.3 cikin 100 na al'ummar kasar, gaba dayansu suna samun walwala da jin dadin rayuwa fiye da yawancin bakar fata ‘yan kasar, in ji gwamnatin na Afirka ta Kudu.
Yawancin gwamnatocin da fararen fata ‘yan Afirka suka jagoranta sun kafa tsarin wariyar launin fata wanda ya hana yawancin 'yancin siyasa da tattalin arziki ga baƙar fata har zuwa lokacin da tsarin ya rushe ta hanyar zabe a shekarar 1994.