Burkina Faso ta bai wa wani kamfanin Rasha na Nordgold lasisin haƙar ma’adinai domin wani aikin haƙar zinari, kamar yadda gwamnatin ƙasar da ke yammacin Afirka ta bayyana.
Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne a yunƙurinta na ƙara samun kuɗin shiga daga ɓangaren zinari a daidai lokacin da farashin zinarin ya yi sama a kasuwar duniya.
Wannan yunƙurin wata alama ce da ke nuna ƙarfin dangantaka tsakanin Rasha da Burkina Faso, a daidai lokacin da gwamnatin sojin ta Burkina Faso wadda ta ƙwace mulki a 2022 ke ƙoƙarin guje wa ƙawayenta na ƙasashen Yamma zuwa Moscow.
Ma’adinar zinari ta Niou, wadda ke a lardin Kourweogo na Burkina Faso, na da girman murabba’in kilomita 52.8 wanda Jilbey Burkina ne ke da lasisin, inda a halin yanzu ya koma hannun Nordgold. Dama can Nordgold na aikin haƙar zinari a Bissa da Bouly.
Majalisar ministoci a ranar Alhamis ta bayyana cewa ana sa ran ma’adinar ta Niou za ta samar da tan 20.22 na zinari a lasisin da aka ba ta na shekara takwas.
Burkina Faso da ke yaƙi da 'yan ta'adda tun shekara ta 2015, ta kasance ƙasa mai arzikin zinari. A cewar wata ƙungiya mai zaman kanta ta Swissaid, wadda ke nazarin haƙar ma'adinai, ƙasar ta samar da fiye da tan 57 a shekarar 2023.
Aikin haƙar ma’adinai na masu ƙaramin ƙarfi
Kamfanonin hakar ma'adinai da ke aiki a wurin sun haɗa da IAMGOLD na Canada da kuma Endeavor Mining, da kamfanin Australia na West African Resource.
Ulf Laessing, shugaban shirin Sahel na gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus ya ce "Haɗin kai da Nordgold da sauran masana’antun haƙo ma'adinai na da muhimmanci (ga gwamnatin Burkina Faso) yayin da ƙasar ke fuskantar matsalar kasafin kuɗi."
Duk da cewa aikin na Niou zai kasance a wani wuri da ƙananan masu haƙar ma’adinai ke aiki, zai hana masu haƙar ma’adinan damar da suke da ita na samun kuɗaɗen amfani, in ji shi.